Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta doke Real Madrid da ci 3-0 a wasan daf da na kusa da ƙarshe na Gasar Zakarun Turai da aka buga a daren Talata a filin wasa na Emirates.
Bayan kashi na farko ya ƙare babu ci, Arsenal ta fito ƙarara a zagaye na biyu inda Declan Rice ya zura ƙwallo biyu a raga, sannan Mikel Merino ya ƙara ta uku da ke bai wa ‘yan Ingila babbar dama kafin karawar dawowa a mako mai zuwa.
A wani wasa da aka buga a daren, Inter Milan ta lallasa Bayern Munich da ci 2-1. Lautaro Martinez ya fara jefa ƙwallon a ragar Bayern, amma Thomas Muller ya rama kafin Davide Frattesi ya ƙara ta biyu ga Inter Milan. Wannan nasara na nufin Inter na da ƙarfin guiwa kafin wasansu na dawowa da za a kara a Italiya.
