Cutar Lassa: NCDC ta tabbatar da ƙarin mutum 14 da suka kamu

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar daƙile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa a makon da ya ƙare daga 24 zuwa 30 ga Maris, 2025, an samu ƙarin mutane 14 da suka kamu da cutar Lassa tare da rasuwar mutane uku. Wannan na cikin rahoton mako-mako da hukumar ta fitar ranar Talata, inda aka bayyana cewa sabbin wanda suka kamu sun fito daga jihohin Ondo, Bauchi, Taraba, Ebonyi da Nasarawa.

NCDC ta ce adadin mace-macen da aka tabbatar ya kai 122 tun daga farkon shekarar 2025 zuwa yanzu, da kashi 18.5 cikin 100 na wadanda suka kamu, wanda ya yi kasa da kashi 18.7 cikin 100 da aka samu a shekarar 2024. Jihohin Ondo, Bauchi da Edo ne suka fi fuskantar annobar, inda aka ce sama da kashi 70 cikin 100 na dukkan waɗanda aka tabbatar sun kamu a bana sun fito daga waɗannan jihohi.

Rahoton ya kuma nuna cewa mafi yawan waɗanda cutar ke kamawa matasa ne ‘yan shekaru 21 zuwa 30, inda aka fitar da matsakaicin shekaru a 30. Haka kuma, maza ne suka fi yawan kamuwa da cutar, da kashi 1.0 ga 0.8 idan aka kwatanta da mata. NCDC ta kuma bayyana cewa cutar ta Yaɗuwa zuwa ƙananan hukumomi 93 a jihohi 18, abin da ke nuna buƙatar ƙarin himma wajen daƙile yaɗuwar ta a faɗin ƙasar.

By ukarofi