Gwamnatin Tarayya ta fito da tsarin binciken ƙasar noma kafin shuka – Mininsta

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin tarayya ƙarƙashin ma’aikatar gona da samar da abinci ta ƙasa ta fito da wani tsarin binciken ƙasa kafin shuka amfanin gona ga manoman Nijeriya, wanda hakan zai baiwa manoma damar shuka abinda ya kamata su gonakin su.

Ƙaramin ministan Gona da samar da abinci Sanata Dr. Aliyu Sabi Abdullahi ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gudana a jami’ar Bayero Kano.

Dakta Aliyu ya ce bayyana cewa wani tsari ne da gwamnatin shugaba ƙasa Bola Ahmad Tunubu ya kawo da za’a bai wa manoma dama a bincika gonar su a gwada a ga me za su iya shukawa kuma a ga wani irin taki ya kamata su saka, domin ya ce kamar likita ne idan aka je asibiti zai auna mara lafiya ya ga abinda ke damunsa to idan an yi gwajin shi ne zai bai wa likita damar fahimtar abinda ke samun mara lafiya, to haka ita ma ƙasa abu ce mai rai a cewar Dakta Sabi.

Ministan wanda ya halacci taron shekara-shekara na ƙungiyar Kimiyyar ƙasa ta Nijeriya wato Soil Science Society of Nigeria (SSSN) wanda shi ne karo na 49 ya gudana ne a Center for Excellence na Jami’ar Bayero, Kano.

Kazalika Dakta Sabi ya ƙara da cewa “Tsarin an riga an fara shi a ƙasashe daban-daban, kuma sun ga amfaninsa, shiyasa muka ce mu ma ba za a bar manomanmu a baya ba, muka kawo wannan tsarin, don a taya manomanmu duban ƙasar noma wanda wannan zai rage asarar da manoma ke yi.

“Mutum zai je ya sayi taki ya je ya barbaɗa a gona ba tare da ya san mene ne gonar ta sa take buƙata ba, to wannan tsarin zai taimakawa manoma ta yadda za su fahimci abinda gonar su take bukata da kuma irin takin da ta ke nema, domin masana sun tabbatar da cewa ba kowace gona ba ce take buƙatar taki wata gonar bata buƙatar taki watakila wata ƙasar kula da ita take buƙata, duk wannan zai fito a wannan tsari ta yadda za’a taimakawa manoma don su bunƙasa abinda suke nomawa wanda idan noma ya bunƙasa za’a samu yawan abinci sai ka ga farashin abinci ya sauka ga ƴan kasa”. inji minista Dakta Sabi.

Taron wanda ya gudana daga Litinin zuwa Laraba, ya samu halartar masana kimiyyar ƙasa na Jihar Kano da ma jihohin ƙasar nan.

By ukarofi