
Daga BELLO A. BABAJI
Karamin Ministan Ayyuka, Muhammad Bello Goronyo, ya naɗa Kwamared Salihu Ɗantata Mahmud a matsayin mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai.
A ranar Alhamis ne aka sanar da naɗin a wata takarda daga Shugaban mai’aikatan ministan, Nafi’u Hussaini Gobir, wanda zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Mayu, 2025.
Ya ce, daga yanzu nauyin kula da harkokin yaɗa labaran ministan da ci-gabansu gami da bada shawarwari kan yadda za’a inganta kimar ma’aikatar a idon al’umma sun koma kan Kwamared Salihu.
Ya kuma yi kira a gare shi da ya kasance mai jajircewa da nuna ƙwarewa wajen sauke nauyin da aka ɗora masa.
Ya ƙara da cewa, an zaɓe shi ne la’akari da gogewarsa na sanin makamar aiki a harkar yaɗa labarai.
