Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Katin Shaidar ɗan ƙasa ta Nijeriya (NIMC) ta gargaɗi ’yan ƙasar da su guji bayyana Lambobin Shaida ta ƙasa (NIN) ga wasu da ba su sani ba, ko wasu ƙungiyoyi, domin kawai a ba su kuɗi.
Gargaɗin ya biyo bayan rahotannin da suka nuna cewa, a na yaudarar wasu mazauna Jihar Anambara su bayar da NIN ɗinsu, domin a ba su kuɗi, abinda hukumar ta bayyana a matsayin “harƙallar da ba ta dace ba”, kuma laifi ne da za a iya hukunta mutum a ƙarƙashin Dokar NIMC mai lamba 23 ta 2007.
A wata sanarwa da Shugaban Sashen Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Dokta Kayode Adegoke, ya fitar a ranar Laraba 9 ga Afrilu, 2025, Hukumar NIMC ta bayyana cewa, an samu rahoto game da wannan haramtacciyar mu’amala, kuma tuni aka kama wasu mutane bisa haɗin gwiwar hukumomin tsaro.
“Hukumar Kula da Shaidar ɗan ƙasa ta ƙasa ta samu rahoton wasu mutane ko ƙungiyoyi da ba su da izini da ke buƙatar mazauna Anambra su miƙa Lambobin Shaidarsu, domin samun kuɗi,” inji sanarwar.
“A kowane lokaci, masu lambar NIN kada su bayar da lambobinsu, don samun kuɗi. Wannan ya saɓa wa dokokin ƙasa. Duk wanda aka kama yana yin haka zai fuskanci hukunci mai tsanani,” inji hukumar.
Hukumar ta NIMC ta kuma sake nanata gargaɗinta na baya, tana kira ga ‘yan Nijeriya da kada su raba NIN ɗinsu ko bayanan su na sirri da wasu da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, saboda hakan na iya jefa su cikin haɗarin satar bayanai da sauran laifukan yanar gizo.
Hukumar ta kuma shawarci jama’a da su riƙa kai rahoto idan sun ga wani yana tattara NIN ba bisa ƙa’ida ba, inda ta buƙaci ayi gaggawar sanarwa ta shafukan hukumar na yanar gizo.
