Garkuwa: ’Yan sanda sun ceto mutum 17 a Kaduna

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Rundunar ‘yan sanda ta ce ta ceto manoman jihar Neja 17 da aka yi garkuwa da su a Kaduna.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, ACP Muyiwa Adejobi ne ya tarbi waɗanda aka ceto a hedikwatar rundunar a madadin Sufeto Janar.

Daga cikin waɗanda aka ceto har da ƙananan yara uku. Nan take aka garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa garin Minna na jihar Neja domin haɗa su da iyalansu.

Aƙalla bindigogi ƙirar AK-47 guda 21 ne aka ƙwato.

Kakakin ‘yan sandan, ACP Adejobi, ya yi nuni da cewa an ceto su ne ta hanyar ba ta dace.

By ukarofi