
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA), ta sauya wajen gudanar da taronta na ƙasa da ta saba yi a kowace shekara daga Jihar Ribas zuwa Enugu, inda ta kafa hujja da taka dokar ƙasa na naɗa jagora, wato ‘Sole Administrator’ don ya shugabanci jihar.
Ta bayyana hakan a matsayin saɓa wa doka biyo bayan sanya dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi tare da nada Ibok-Ette Ibas (mai ritaya) a matsayin jagoran a watan Maris.
A sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis ƙarƙashin Shugabanta, Mobolaji Ojibara, NBA ta yi alla-wadai da tsarin shugabancin da ke gudana a Ribas sakamakon bijire wa tsarin da dokar ƙasa ta bada dama a ƙasar na amfani da tsarin demokraɗiyya.
Ta ce, kodayake Majalisar Dokoki ta amince da hukuncin Shugaban ƙasar, amma yin hakan ba daidai bane kasancewar ya saɓa wa sashe na 11 da na 188 na kundin dokar ƙasa.
A saboda haka ne ta yanke shawarar sauya wajen taron nata zuwa Enugu, babban birnin Jihar Enugu, ta na mai kira ga ɗaukacin mambobinta da su bada haɗin-kai wajen tabbatar da nasara ga tafiyarsu.
