Wasu da ba a san ko su waye ba sun sace wata mota kirar Toyota Hilux mai launin baƙi mallakin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA), Nuhu Ribadu, a Abuja yayin sallar Juma’a.
Rahotanni sun ce an ajiye motar ne da misalin ƙarfe 1:05 na rana kusa da ginin hukumar ƙaramar hukumar birnin Abuja (AMAC) da ke Area 10, inda jami’in ofishin ya shiga masallaci domin sallar Juma’a.
A cewar Zagazola Makama, wani ya wallafa labarin a shafinsa na X (tsohon Twitter), jami’in ya fito daga masallaci sai ya tarar babu motar da ya ajiye.
An ce an sanar da sashen ‘yan sanda na Garki da misalin ƙarfe 2:00 na rana, kuma nan take jami’an tsaro suka fara ɗaukar matakin bincike.
Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya ta kaddamar da matakan tsananta bincike a shingayen bincike da kuma kulle hanyoyin shiga da fita daga birnin domin gano masu laifin da dawo da motar.
Kakakin rundunar ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana ci gaba da gudanar da bincike don cafke masu laifin da kuma dawo da motar da aka sace.
