
Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon mawaƙin Hip-hop na Nijeriya, Eedris Abdulkareem ya ce wani Sanata a Nijeriya ya masa tayin cin hancin Naira miliyan 200 bisa sabuwar waƙar da ya fitar, wadda aka yi wa laƙabi da ‘Tell Your Papa’.
A wanin bidiyo, mawaƙin ya ce an masa tayin ne da sunan tallafa wa yunƙurinsa na samar da sabuwar taken zanga-zanga.
Lamarin ya biyo bayan haramta waƙar da Hukumar Kula da Watsa Labarai (NBC) ta yi kwanaki kaɗan da fitar da ita.
Ya ce, ya samu kira daga wani da ya yi ikirarin cewa shi Sanata ne, wanda ya ce masa sun yi zama da Seyi Tinubu da wasu jami’an gwamnati, waɗanda ke shirin kiran sa da nufin ba shi cin hanci.
Ya faɗa wa mawaƙin cewa kada ya amince da buƙatarsu, ya na mai bayyana masa cewa za su riƙa ɗaukar nauyinsa ta ƙarƙashin ƙasa.
Saidai, mawaƙin ya ce bai amince da tayin ba kasancewar bai san daga ina ko wace manufa ta sa aka neme shi da hakan ba.
A ranar 10 ga watan Afrilu, 2025 ne NBC ta sanar da haramta waƙar ta ‘Tell Your Papa’ wadda ke ƙalubalantar jagorancin Shugaba Tinubu da halin tsadar rayuwa da al’umma ke fama da ita a ƙasar.
Lamarin da ya haddasa rashin amincewa acikin ƙungiyoyin al’umma da masu-ruwa-da-tsaki a masana’antar waƙa.
