An karrama shugaban Qausain TV, Kanar Sani Bello da lambar yabo

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Maigirma Shugaban Gidan Talabijin na Qausain TV, da kuma kamfanin makamashi na Mainstream Energy Solutions Limited (MESL) Kanar Dr. Sani Bello (Mai ritaya) ya samu lambar yabo ta nasarar rayuwa a fannonin Kasuwanci, jagoranci da karamci daga cibiyar haɗin gwiwa ta Nigerian-American Chamber of Commerce (NACC).
An karrama Kanar Bello ne a yayin bikin cikar cibiyar shekaru 65 jiya a Legas, inda cibiyar ta aminta da gagarumin jagorancinsa ga ƙwararrun ‘yan kasuwa da kuma fitattun gudummawar da ya taimaka wa harkokin kasuwanci, da kafofin yaɗa labarai, da makamashi na Nijeriya.
Hakazalika a ƙarƙashin jagorancinsa, kamfanin makamashi na MESL ya samu nasarar sarrafa manyan tashoshin samar da wutar lantarki kamar Kainji, Jebba, Zungeru, da Kashimbila, yayin da Gidan talabijin na Qausain yake cigaba da bunƙasa a matsayin babbar murya a ɓangaren yaɗa shirye-shirye.
Bikin ya kuma gabatar da naɗin Alhaji Sheriff Balogun a matsayin shugaban majalisar na ƙasa karo na 20, ƙarƙashin taken: “Alfanun haɗin gwiwa: Shekaru 65 na inganta dangantakar tattalin arzikin Nijeriya da Amurka.”
Hukumar ta NACC ta ci gaba da jajircewa wajen inganta dangantakar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Nijeriya da Amurka.

By ukarofi