Harin sojin sama ya kashe kwamandan ISWAP da wasu ‘yan ta’adda 100 a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Wani babban kwamandan ‘yan ta’adda da aka fi sani da Gwaska, ya baƙunci lahira sakamakon harin da sojin sama na Najeriya suka kaiwa dabarsa.

Gwaska wanda rahotanni suka bayyana cewa shi ne na biyu a girman muƙami a ƙungiyar ISWAP, an kashe shi tare da wasu ‘yan ta’adda 100 a wani samame da sojoji suka kai a Jihar Katsina.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na Jihar Katsina Dakta Nasir Mu’azu ne ya bayyana wannan nasara da jami’an tsaron suka samu.

Sanarwar ta ce, “A ranar 10 ga Afrilu, 2025, rundunar sojojin Najeriya ta 17 wato 17th Brigade da kuma rundunar 213 Forward Operating Base (FOB) ta rundunar sojojin saman Najeriya sun kai wani gagarumin hari a yankunan Mununu Bakai, Zango, Jeka Arera, Malali, da Ruwan Godiya da ke ƙananan hukumonin Faskari da Ƙanƙara.”

Kwamishinan ya ce an gudanar da aikin ne bisa samun ingantattun bayanan sirri kafin kai harin kan muhimman maɓoyar ‘yan ta’addar da suke amfani da ita wajen aikata laifi.

Ya ƙara da cewa, “Sahihancin aikin, bisa la’akari da bayanan sirri, ya kawar da wani ƙasurgumin ɗan ta’adda da ake kira Gwaska, wanda ya yi aiki a matsayin shugaba na biyu ga wani shugaban ‘yan ta’adda da ake alaƙanta da ƙungiyar ISWAP.”

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa kwanan nan Gwaska ya tashi daga ƙaramar hukumar Ɗanmusa zuwa dajin Mununu, inda aka gano shi aka kuma kashe shi.

“A yayin samamen, sojojin sun ƙwato tare da lalata manyan bindigu guda biyu, da wasu bindigu da aka ƙera na gida, da sauran makamai domin hana sake amfani da su daga masu aikata laifuka,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa wannan aiki da aka samu nasarar sa ya yi mummunar illa ga ƙungiyoyin da ke addabar al’umma a ƙananan hukumonin Faskari, da Ƙanƙara, da Bakori, da Malumfashi, da kuma Ƙafur.

By ukarofi