Ya lakaɗa wa ɗiyarsa duka har lahira

Spread the love

Wani magidanci ya shiga hannun hukuma bayan da ya lakaɗa wa ’yarsa mai shekaru 27 duka har lahira a yankin Ojo da ke Jihar Legas.

Kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa rundunar ta cika hannu da magidncin ne bayan ya yi aika-aikan a ranar 3 ga watan nan na Afrilu.

Hundeyin ya ce makwabta ne suka kwarmata wa Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke yankin Okokomaiki, bayan mutumin ya kashe ’yar tasa ya kuma binne ta a cikin harabar gidansu.

Jami’in ya ce, “Bayan samun rahoto jami’anmu suka ce suka gano kabarin, suka tono gawar aka gudanar da bincike,” shi kuma yana hannun hukuma yana amsa tambayoyi.

By ukarofi