Daga MAHDI MISA MUHAMMAD
A ci gaba da kai hare-hare kan masu aikata laifukan satar man fetur, dakarun runduna ta 6, na sojojin Nijeriya, sun ci gaba da matsin lamba ga masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa a yankin Neja Delta.
A cikin ayyuka da yawa da aka gudanar tare da sauran hukumomin tsaro a faɗin yankin JOA daga ranar 31 ga Maris zuwa 6 ga Afrilu, 2025, sojoji sun samu ci gaba mai yawa, wanda ya haifar da kama mutane 43 da ake zargin satar mai da laifuffukan da ke da alaƙa da su, da lalata haramtattun matatu 14, ruguza jiragen ruwa 14 da aka yi amfani da su wajen satar mai tare da kama motoci da yawa maƙil da litar mai 254,000.
Wata sanarwa da muƙaddashin daraktan hulɗa da jama’a na runduna ta 6, Laftanar Kanal Danjuma Jonah Danjuma ya fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa, a wani samame da aka gudanar a jihar Delta, sojojin sun gano wani katafaren wurin da ake tace mai ba bisa ƙa’ida ba a Old Ogorode a ƙaramar hukumar Sapele.
Sanarwar ta ce, an kwato kayayyaki da dama a wurin, waɗanda suka haɗa da mota kirar Ford Bus mai lamba Delta KLK 797 HR, ɗauke da ganguna 9 na lita 1,000 kowannen su ya cika da lita 90,000, ganguna 74 na lita 200 kowanne ya tanadi 14,800, da tanki guda na sama da lita 20,000.
