Matan Aure: Garin neman gira..

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Idanuwan mata da yawa sun karkata kan fassara ma’anar aure a matsayin kwanciya da miji har ya ji ya rikice don ni’imar ki. Hakan kan sa su bauta wa kayan mata da duk abin da su ka mallaka.Yayin da idanuwansu kan rufe, su kan ka sa bambance tsakanin kayan ni’ima da kayan illa. A wannan shafi na iyali, a watan makon zan yi amfani wurin janyo hankalin mata ne kan amfani da itatuwa da sinadarai barkatai da sunan ƙarin ni’ima. Abin al’ajabi kaso mafi yawa na kayan da muke amfani da su ba mu da masaniyar abubuwan da ke cikinsu. 

Bari mu fara daga in da mu ka sani; shin ba ki taɓa cin karo da kayan mata da ki ka sha ya dawo da al’adar ki ba? Ko ba ki taɓa shan wanda ya sanya ki gudawa ba? Ko ya sanya ki zubar ruwa amma ba farare ba? Ko ya sa ki zazzaɓi? Wani lokacin idan akwai ciki wadda ta sha cikin ya zube? Shin ba ki taɓa cin karo da ɗan matsi da idan kin yi amfani da shi za ki ji tamkar ki yi ihu saboda tsananin zafi? Duk waɗannan su na ɗauke da alamar tambaya wanda ya kamata mu yi nazari kafin a sanar da mu. Da yawa a cikin masu sayar da hakin maye (kayan mata) ba masana itatuwa ba ne. Hakan zai sa a yi maki ‘rabka Tanin bisa Rakkiya’ a ba ki. Ke kuwa saboda idonki a rufe yake ba bincike za ki auna a cikinki. 

Akwai kayan matan da ke da ɗaci duk da cewa an haɗa su da wasu da za su rage kaifin. Kin taɓa tambayar a cikin itatuwa masu ɗaci wanne ne daga ciki mai amfanin ko mai illa? Ku na da masaniyar akwai cututtuka da dama da mace kan haɗu da su ta sanadiyyar shan kayan mata barkatai? Ciki kuwa har da ciwon daji na mahaifa ko na farji.

Ba wai ina ƙoƙarin hana mata amfani da kayan mata ba, ko nuna shan su bai kamata ba bakiɗaya, abinda nake ƙoƙarin faɗa a nan shi ne, idan za a sha a tabbatar da sahihancin sa ta hanyar fara sanin ko akwai abinda zai iya illata ki a ciki. Sanin tsafta da ƙwarewar wadda ta siyar maki da shi. Idan hakan ta samu, ku yi ta sha har sai kun gode Allah, ku ta adashen da ba kwasa akansu domin biyan buƙata ya fi dogon buri.

Saidai abin takaici wasu matan ma ba don Allah suke shan maganin ba. Kawai su na sha ne don su mallake miji, hakan ke sanya su kauce hanya, wato shirka ba tare da sun sani ba. Dalili yanzu malamai sun tashi tsaye wurin yi wa mata nasiha tare da lurar da su haramcin zuwa wajen bokaye da ‘yan bori. Kuma alhmdu lillahi an yi nasarar karkatar da mata da yawa zuwa ga hanya madaidaiciya. Sai dai a wurin bokayen sukan ce in sun san wata to fa ba su san wata ba. Da yawa suka haɗa ‘yan komatsan su suka yi hijira zuwa cikin gari, suka bar daji, inda suke juya akalar bokancin su zuwa bada maganin mata. Dalilin su kuwa, mata sun mayar da kansu ‘yan maye na kayan mata, neman sa suke yi ruwa jallo. Ba ma kamar idan an ce masu na mallaka ne.Tambayar da zan yi wa mata, idan ki ka mayar da kowane irin kayan mata a cikinki, mijina rawar kai akan ki, har yana koɗa ki tare da haska ki a matsayin tauraruwar sa. Ranar da suka yi sanadiyar lalacewar ki zai zauna da ke? Ko zai ce tun da a baya ya wadatu da ke yanzu zai yi haƙuri da ke a hakan, ba wulakanci ba kishiya? Abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa; ba na jin za a yi tafiya mai nisa ɗayan biyu zai faru, ko dai ya sake ki, ko ya danƙaro miki kishiya su ciyar da ke tuwon baƙin ciki, kin ga kuwa wa gari ya waya? Garin neman gira an rasa idanu.

By ukarofi