Duk yanda na so kau da ido kan yanda sabon yaƙin da Isra’ila ta ƙaddamar kan Gaza sai na ga ba zai yiwu ba don yadda sojojin ke fakewa da kai hari kan ‘yan Hamas amma haƙiƙa jama’a da ba ta yi wa kowa laifi ba harin ke shafa. Mutane na cikin gidajen su sai a jefa mu su bom su mutu. Akwai ma gidan da yara ke wasa a ka harba mu su makami mai linzami shikenan sai gawar su a ka samu. Bayan wasu hare-haren ma sai an tona ƙasa ko ruguzazzun konkere kafin a samo gawar mutane. Duk maganar da Hamas ke yi na damuwa kan abun da ke faruwa tamkar ba da duniya ta ke magana ba saboda ai Isra’ila ta zayyana ta a matsayin ƙungiyar ‘yan ta’adda. Wannan shi ne ga mari ga tsinka jaka ko a ɗaki mutum a hana shi kuka. Gaskiyar magana daga abun da na lura da shi tun lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya dau matsayar kaurar da ‘yan Gaza daga garuruwan su da hakan ya samu turjiya sai ya zama tamkar an yanke mu su hukuncin kisa ko duk abun da ya same su su su ka ja wa kan su. Za ka ji ba wata kwakkwarar adawa daga turai kan sabon babin zubar da jini da a ka shiga tun wargajewar yarjejeniyar tsagaita wuta a watan jiya. Dama ai Isra’ila na da lasisin kashe Falasɗinawa da nuna hakan kare kai ne. A hotuna har ma fayafayan bidiyo an sha ganin inda Falasɗinawa ke jifa da duwatsu yayin da sojojin Isra’ila ke amfani da tankokin yaƙi ko manyan bindigogi shake da albarusai don kashe duk wanda tsautsayi ya faɗa kan sa. Har yau fa ba abun da a ka yi kan jinin ‘yar jarida Bafalasɗiniya da sojojin Isra’ila su ka bindige. Shireen Abu Akle na sanya da falmara da rubutu gwara-gwara PRESS da ke nuna ‘yar jarida ce amma haka sojojin Isra’ila su ka buɗe ma ta wuta su ka yi ma ta kisan gilla. Da farko sun ma musanta aikata hakan sai da ta baiyana ta na aiki ne da sashen Larabci na gidan talabijin ɗin Aljazeera. Tun da ta na cikin Falasɗinawa jinin ta ba shi da wani daraja. Sharhin lamarin ya nuna da gangan a ka kashe ta don yadda ta ke aika rahotanni daga sansanonun Falasɗinawa da ke cikin ukuba. Kisan ya auku ne a yankin Jenin. Duk wanda ya duba batun yaƙi kan Gaza cikin adalci zai iya fahimtar Isra’ila ta ki jinin duk wani batu na samun ‘yancin Falasɗinawa ta kafa ƙasar su mai babban birni a gabashin Kudus. Isra’ila na son dauwamar ƙasar Falasɗinu a ƙarƙashin mulkin mallaka ko ma ya zama yankin ‘yan bora na Isra’ila. Don haka duk wanda ya taso da gwagwarmayar tabbatar da ‘yancin yankin kai tsaye ya shiga bakin littafin Isra’ila kuma zai fuskanci hukuncin kisan da ba sai an shiga kotu ba Tsarin irin gwamnatin jeka na yi ka ta Falasɗinawa da ke birnin Ramallah ne ka iya zama dama-dama don kawai makamin gwamnatin da ke karkashin shugaba Mahmud Abbas shi ne nuna fushi ko yin Allah wadai.
Kazalika Ramallah na matukar kin jinin Hamas da ma taya Isra’ila caccakar kungiyar fafutukar. Abu daya dai gaskiyar magana ‘yan diflomasiyyar Falasɗinawa a sassan duniya na bakin ƙoƙarin kare muradun dukkan Falasɗinawa ba tare da wariya ba.
In mun duba bambabcin gwamnatin tsohon shugaban Amurka Joe Biden da ta Trump shi ne a yayin da Biden ke rara gefe wajen nuna ya na son sulhunta sassan biyu don da dubawa Isra’ila makamai don yaƙi da Falasɗinawa, Trump gaba ɗaya buƙatar Gazawa ya yi su tashi daga ƙasar su ta gado. Hakanan yayin da Biden ke hawa kujerar na ji wajen matakai kan Isra’ila a Majalisar ɗinkin Duniya, Trump har barazana ya ke yi ga duk ƙasar da ta mara baya ga al’ummar Gaza. Trump da a ke ganin ba ya son kashe kuɗin Amurka wajen yaƙi maimakon bin matakai adalci ga Falasɗinawa sai ma ya kaddamar da yaƙi kan Houthi a Yaman. Idan an samu sulhu a fitinar me zai sa Houthi kai hari kan jiragen dakon man fetur na ƙasashen da ke marawa Isra’ila baya a Bahar Maliya. Saudiyya da sauran ƙasashen Larabawa na nanata matakin zaman lafiya na kafa ƙasar Falasɗinu a gefen Isra’ila da a ka tsara gabanin shekarar 1967 amma sam magoya bayan Isra’ila ba sa son jin maganar ko ma ba sa tattauna batun sam.
Da alamu sojan Isra’ila na neman sauya matsaya kan kisan gilla da su ka yi wa jami’an lafiyar Falsɗinawa 15.
Da farko sojojin sun ce motocin jami’an lafiya na tafiya ba tare da wutar alamar aiki ta gaggawa ba kuma su na nufar sojojin Isra’ila da ke kusa.
Fitowar faifan bidiyo da ya nuna wuta karara da tafiya cikin natsauwa ta jami’an lafiyar ya sa sojan na Isra’ila nuna kuskure a ka samu kuma na ƙaddamar da bincike.
Bayan buɗewa jami’an lafiyar wuta da kashe su sai mota BULLDOZER ta Isra’ila ta markaɗe su da bunne su a wani babban kabari.
Shugaban ‘yan agajin Red Crescent a Gaza Marwan Jilani ya ce an samu faifan bidiyon a aljihun ɗaya daga jami’an da Isra’ila ta kashe.
An ji sautin wanda ya dau faifan kafin a kashe shi ya na neman mahaifiyar sa ta yafe ma sa don wannan hanyar ta taimakon jama’a ya zaba a rayuwar sa ga shi hakan ya yi sanadiyyar rasa ran sa.
Bayan kwana 4 da bunne jami’an ne a ka samu damar isa bigiren a ka tono su don jana’izar da ta dace.
Mummunan harin da sojojin Isra’ila su ka kai kan wani ginin mazaunin jama’a a Gaza ya yi sanadiyyar mutuwar Falasɗinawa 23.
Harin kamar yanda rundunar kiyaye farar hula ta bayyana ya auku ne a Shujaiya kuma akasarin wanda su ka rasa rai mata ne da ƙananan yara.
Shugaban rundunar Mahmud Bassal ya ce harin ya haɗa da kashe mata 8 da yara 8 inda fiye da mutum 60 kuma su ka samu raunuka.
Akwai mutane da dama da a ke ta fafukar nema da gini ya danne su da ba a tantance halin da su ke ciki ba.
Ganau ya ce an harbo makamai masu linzami da dama kan ginin mai hawa huɗu inda karafan makamai su ka yi ta faɗawa sassa.
Ganau ɗin mai suna Ayyub Salim ya ce kura ta turnuke inda naman jikin waɗanda a ka kashe ya tarwatse.
Wajen na da mutane da dama da su ka haɗa da waɗanda ke samun matsuguni bayan rasa gidajen su.
Sojan Isra’ila sun ce sun auna wani babban dan ƙungiyar mayaƙan Hamas ne a ginin.
Hamas ta yi Allah wadai da harin da bayyana cewa ya na daga kisan kare dangi da gwamnatin Yahudawa ke yi kan Falasɗinawa.
Harin Amurka na Sanaa ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 4 – Houthi:
ƙungiyar mayaƙan Houthi a Yaman ta bayyana cewa harin da Amurka ta kai kan babban birnin ƙasar Sanaa ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 4.
Houthi dai na riƙe da sassa da daman a Yaman tun 2014 ciki da babban birnin ƙasar inda su ke mulki.
Wannan na nuna cigaba da hare-hare da Amurka ke kai wa kan sassan da ke ƙarƙashin Houthi don dakile hare-haren da mayaƙan ke cillawa kan jiragen ruwan kasashen da ke marawa Isra’ila baya da ke zirga-zirga a Bahar Maliya.
Faifan bidiyon da da shugaban Amurka Donald Trump ya sake na nuna harin ya kashe fiye da mutanen da Houthi ta bayyana.
Hakanan Trump ya saki wani bidiyo da ke nuna wasu mutum fiye da 70 sun taru inda a ka jefa mu su bom da Trump ya zaiyana da an gama da su ba za su sake kai hari ga Amurka ba.
Houthi dai ba ta ambaci hari ya shafi wasu daga dakarun ta ba.
Ma’aikatar lafiyar Houthi ta kara da cewa harin na Amurka ya faɗa kan wani gida inda ya raunata mutum 16.
Tun fara kai hare-haren bisa umurnin Trump an yi kiyasin Amurka ta kashe mutum 69 a yankunan na Houthi da su ka haɗa da Saada.
Kammalawa;
Duniya dai na gani ga halin da Falasɗinawa ke ciki na kisa kuma kullum lamarin ƙara ta’azzara ya ke yi. Shin ina adalcin duniya ne? ko dai ba adalci yanzu? A zahiri Isra’ila na son ƙarar da Falasɗinawa ne ko karya lagon duk wani da zai iya ce ma ta kanzil. Tarihi ya nuna zalunci ba ya dauwamar har abada duk tsawon dare gari zai waye. Duk wani mataki na tabbatar da adalci ba zai yi kaɗan ba. Shawara mai kyau ko ziyarar ofisoshin jakadancin Falasdinawa na ƙasashen da ke kusa don ba da goyon baya na da amfani. Tayawa da daga murya ta hanyar rubuce-rubuce ko sauran hanyoyi na kafafen labaru na da tasiri. Yankin Gaza ne ya zama kangaye da al’umma ke zaune don kare martabar ƙasar su ta gado. Duk Dan Gaza na nuna alamun burin sadaukar da kan sa don Gazawa da ke zuwa a gaba su samu rayuwar ‘yanci. Ban da tsoro don hakan ma ba shi da amfani tun da mutum ya na cikin gidan sa ma za a jefo ma sa bom.
