Arsenal ta yi waje da Madrid a Champions League

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta yi nasarar hayewa zagayen wasan kusa da na ƙarshe a Gasar zakarun Nahiyar Turai, wato Champions League a karo na uku a tarihinta, bayan doke Real Madrid da ci 2 da 1 a filin wasa na Santiago Bernabeu.

Hakan ya bata damar yin nasara akan Madrid da jimillar ci 5 da 1 bayan da ta doke ta da ci 3 da 0 a karawar farko, makon da ya gabata.

Ɗan wasa Bukayo Saka ne ya zura ƙwallo a minti na 65 wanda hakan ya ƙara wa Arsenal ƙwarin gwiwa, inda bayan minti biyu da haka ne, Vinicius Junior na Madrid ya farke sakamakon kuskure da ɗan wasan bayan na Arsenal, William Saliba ya yi.

Ana daf da tashi ne a mintinan ƙarshe, ɗan wasan gaba na Arsenal, Gabriel Martinelli ya zura ƙwallo ta biyu a raga.

Da farko dai Arsenal ta samu bugun fenareti, wanda Saka ya zubar mata sakamakon ture ƙwallon da golan Madrid, Thibaut Courtois ya yi.

A yanzu dai Arsenal za ta fafata da ƙungiyar PSG, wato Paris Saint Germain ta ƙasar Faransa, yayin da Inter Milan kuma za ta kara da Barcelona.

Wannan shi ne karo na farko da Arsenal ta kai zagayen wasan dab da na ƙarshe a gasar tun shekarar 2009, a lokacin da ya yi waje Villareal.

By Babaji