
Daga BELLO A. BABAJI
Gwamnatin Jihar Ribas ta musanta batun gayyatar dakataccen Gwmana, Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Udo zuwa wani zama da aka shirya gudanarwa a Gidan Gwamnatin jihar a ranar 18 ga watan Afrilu, 2025.
Ta ce, labarin bai inganta ba kuma ba daga sahihin madogara ya fito ba.
A ranar Litinin labarin gayyatar ya karaɗe kafafen sadarwa, inda aka ce Jagoran Gwamantin jihar, VA Ibok-Ete Ibas ya sanar da yin zama da Fubara da mataimakiyar tasa.
Saidai, Baban Sakataren Ayyuka na Musamman daga ofishin sakataren Gwamnatin jihar, Dede Sampson Friday, ya yi kira ga al’umma da su ƙaurace wa rahoton.
Ya ce, an ƙirƙiri batun ne da nufin haddasa rikici daga wasu da ke adawa da zaman lafiya, waɗanda ke ƙoƙarin ruɗar da al’umma.
Ya kuma ce, ana samun bayanan gwamantin jihar ne ta sahihin ofisoshi da shafukan labarai da ta amince da su.
