HOTUNA: Yadda aka gudanar da bikin ƙaddamar da aikin gyaran hanyar Abuja-Kaduna

Spread the love

An gudanar da bikin ƙaddamar da aikin gyaran hanyar Abuja-Kaduna a hukumance, wanda ya samu halartar wakilin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu GCFR, Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani.

Taron ya kuma samu halartar ministan qyyuka, Injiniya Dave Umahi, da ƙaramin minista na ma’aikatar ayyuka, Barista Bello Muhammad Goronyo, da sauran manyan baƙi daga sassa daban-daban na gwamnati.

Aikin gyaran yana daga cikin matakan gwamnatin tarayya na tabbatar da ingantattun hanyoyi da tsaro ga masu zirga-zirga tsakanin babban birnin tarayya da Arewacin ƙasar.

By ukarofi