Obasanjo, Jonathan da Buhari ne tushen ƙarancin lantarki a Nijeriya – Gwamnatin Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya ɗora alhakin rashin ci gaban da aka samu a ɓangaren lantarki a kan gwamnatocin da suka shuɗe ƙarƙashin shugabancin Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari, yana mai cewa ƙoƙarin da aka yi a baya na kawo sauyi a fannin bai haifar da ɗa mai ido ba

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya bayar da rahoton cewa, ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar Bankin Duniya a ofishinsa da ke Abuja ranar Laraba.

A cewarsa, an daɗe ana watsi da ababen samar da wutar lantarki daga shekarar 1999 zuwa yau, wanda hakan ya taimaka wajen rugujewar wannan fanni.

Idan za a iya tunawa, tuna Olusegun Obasanjo, Umaru Yar’Adua, Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari su ne shugabanni a lokacin da aka ambata.

Adelabu ya ƙara da cewa, “A gaskiya muna da abubuwan da ba mu yi alfahari da su ba, a cikin shekarun da suka gabata, muna ba da gudunmawa ne kawai don kawo sauyi a fannin samar da wutar lantarki, ba mu yi aiki da magana ba, gwamnatocin baya a cikin shekaru 25 da suka gabata sun ci gaba da yin irin wannan abu a kowane lokaci kuma ba za ku iya samun sakamako daban-daban a kan hakan ba, wanda shi ne dalilin da ya sa muka yanke shawarar yin abubuwa daban-daban a wannan karon.

By ukarofi