Kotu ta saki yaron da ya tare motar Peter Obi bayan watanni a tsare

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kotun Majistare da ke Apapa a Orege, Ajegunle – Sikiru Adagun Courthouse, ta sallami Alabi ƙuadri tare da wanke shi.

An fara ganin Alabi ne a lokacin zaɓen 2023 bayan da wani hotonsa tsaye a gaban ayarin motocin yaƙin neman zaɓen Peter Obi a Legas ya riƙa yawo a shafukan sada zumunta.

An sallame shi tare da wanke shi daga zargin haɗa baki da aikata laifi da kuma fashi da makami. Kotun ta ce, ba shi da wata ƙara da zai amsa.

An gurfanar da ƙuadri a kotu a ranar Alhamis 17 ga Afrilu, 2025, bayan ya shafe watanni a gidan yarin Kirikiri da ke Legas.

Hukumar Kula da Gidan Gyaran Hali Nijeriya ta gabatar da ƙuadri a Kotun Majistare ta Apapa, da ke Orege, Ajegunle, Kotun Sikiru Adagun (Kotu ta 9).

An fara sauraron ƙarar ƙuadri a ranar 28 ga Afrilu, 2025. Sai dai lauyan kare haƙƙin ɗan Adam kuma mai fafutuka Inibehe Effiong ya bayyana cewa shi da Daraktan ƙararrakin jama’a (DPP) sun buƙaci a ci gaba da wannan ranar, kuma kotun ta amince da buƙatar.

Effiong ya bayyana cewa an ɗaure Alabi a cikin gidan yarin Nijeriya ba gaira ba dalili saboda wani laifi da wasu ‘yan iskan gari suka yi a unguwarsu.

Effiong, wanda kwanan nan ya ziyarci Kotun Majistare ta Apapa da ke Legas tare da mahaifiyar Alabi da kuma abokan aikinsa na lauya, ya bayyana cewa tafiyar Alabi zuwa gidan yarin Kirikiri ba wai kawai abin ban haushi ba ne, amma ga alama bita-da-ƙulli saboda baƙin cikin tallafin kuɗi da Alabi ya samu bayan yaƙin neman zaɓen 2023.

Effiong ya bayyana cewa an kama Alabi ne a watan Janairu a kusa da gidansu a lokacin da yake dawowa daga aiki.

Ana zargin sun kai shi ofishin ‘yan sanda na Amukoko (wanda aka fi sani da ofishin ‘yan sanda na Pako) inda suka zarge shi da hannu a faɗan titi.

Sai dai kuma, Alabi ya gurfana a gaban wata kotun majistare tare da wasu mutane huɗu, waɗanda aka ce sababbin fuskokin ne a gare shi, bisa zargin haza baki wajen yin fashi da makami tare da adda.

A cewar takardar tuhumar, an yi wa waɗanda ake abin ya shafa fashin kuɗi N579,000, da wayoyin hannu huɗu.

By ukarofi