An kai hari gidan iyayen Sanata Natasha a Jihar Kogi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wasu ɓata-gari ɗauke da bindigogi da takubba sun kai farmaki gidan iyayen Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Matasan sun kai hari gidan da ke unguwar Obeiba-Ihima a ƙaramar hukumar Okehi ta jihar Kogi ne a safiyar ranar Talata.

Majiyoyin tsaro sun shaida cewa Babban Jami’in Tsaron Sanata Natasha, Yakubu Oɓanja, ne ya kai rahoton harin ga hukumomin tsaro.

Oɓanja ya bayyana cewa, harin ya afku da misalin ƙarfe 1:00 na dare, inda aƙalla mutane uku ɗauke da makamai suka lalata ginin gidan har da farfasa tagogi.

Rahoton ya ce, bayan samun kiran gaggawa, tawagar jami’an tsaro daga rundunar ‘yan sanda ta Okehi sun garzaya zuwa wurin da abin ya faru cikin gaggawa.

Babu wanda aka ji wa rauni ko aka kashe, kuma ba a samu kama ko ɗaya daga cikin masu farmakin ba, amma an ɗauki bayanai daga wurin, domin fara bincike a mataki na farko.

Majiyoyin ’yan sanda sun bayyana cewa, ba a tabbatar da dalilin kai harin ba tukunna yayin da bincike ke ci gaba.

Sanata Akpoti-Uduaghan, wacce fitacciyar ’yar siyasa ce a yankin Kogi ta Tsakiya, ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto.

A baya-bayan nan, Sanata Natasha Akpoti ta yi zargin cewa, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, yana da hannu wajen kitsa wani yunƙuri na kashe ta a ƙaramar hukumarta.

Yayin dawowarta gida domin ganawa da mutanenta, Natasha ta shaida musu cewa, Akpabio ya haɗa baki da Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello, domin kashe ta.

Ta ƙara da cewa, sun shirya ɗora wa al’ummar mazaɓarta laifin kisan nata, duba da yadda rikici ke ƙara dagule wa tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa.

By ukarofi