Haɗaka: Bayan tutsun gwamnonin PDP, ɓangaren CPC sun bayyana goyon bayan Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Bangaren rusasshiyar jam’iyyar CPC, wacce ta kasance ɗaya daga cikin jam’iyyun da suka haɗu suka kafa jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya a yanzu, ta kaɗa ƙuri’ar amincewa da ci gaba da mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya.

CPC dai ta kasance tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne a matsayin jagoranta kafin haɗewarta da jam’iyyar APC.

Wannan mataki na ’yan rusasshiyar jam’iyyar CPC ya zo ne bayan da ɓangaren babbar jam’iyyar adawa ta Nijeriya, PDP, aka samu ƙungiyar gwamnoninta sun sanar da cewa, ba za su yi haɗaka da kowacce jam’iyya a Nijeriya ba, makamanciyar haɗakar da jam’iyyun CPC suka yi a 2014 suka kafa APC, wacce ta lashe zaɓen 2015.

Tun bayan sauya sheƙar ɗaya daga cikin mambobin CPC kuma tsohon Gwamnan jJihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai zuwa jam’iyyar Social Democratic Party, SDP, aka fara nuna damuwa kan yadda CPC a jam’iyyar APC za ta fuskanci batun shirin ficewa daga jam’iyyar mai mulki.

ƙungiyar, a cikin wani ƙuduri ranar Laraba ta ce, “Labarin yaudara na baya-bayan nan da ke nuni da sauya sheƙa ko rashin gamsuwa a tsakanin masu ruwa da tsaki na CPC ba su da tushe, barna, kuma ya kamata a yi watsi da su.

“Muna ci gaba da kasancewa muhimmin ɓangare na jam’iyyar APC, mun jajirce wajen gudanar da jagoranci da hangen nesa.”

Waɗanda suka rattaɓa hannu kan ƙudurorin sun haɗa da tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Umaru Al-Makura; tsohon Gwamnan Jihar Katsina kuma tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Alhaji Aminu Masari; tsohon Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu; Sanata Ibrahim Musa, Sanata Mustafa Salihu, Hon. Farouk Aliyu Adamu, Almajiri Geidam, Waziri Bulama, Dr. Nasiru Argungu da Dr. Dominic Alancha.

Sauran sun haɗa da Ayuba Balami, Mista Osita Okechukwu, Cif Okoi Obono-Obla, Lucy Ajayi, Captain Bala Jibrin, Uche Ufearoh, Alhaji Yusuf Salihu, Abubakar Maikuɗi, Injiniya Mutallib Badmus, Alhaji Muhammed Datti, Muhammed Etsu, Chief Jerry Johnson da Alhaji Alƙali Ajikolo.

Wani ɓangare na ƙudirorin ya ƙara da cewa, “mu shugabanni da muka rattaɓa hannu a kai, da kuma ’yan rusasshiyar jam’iyyar CPC, waɗanda suka taka rawa wajen haɗewar jam’iyyar APC mai cike da tarihi, mun fitar da wannan sanarwa ne domin tabbatar da biyayyarmu ga babbar jam’iyyarmu da kuma nuna goyon bayanmu ga Gwamnatin Shugaba Tinubu.

“Labarin yaudara na baya-bayan nan da ke nuni da sauya sheƙa ko rashin gamsuwa a tsakanin masu ruwa da tsaki na CPC ba su da tushe balle makama, kuma ya kamata a yi watsi da su, mun ci gaba da kasancewa wani muhimmin ɓangare na jam’iyyar APC, mai cikakken himma ga shugabancinta da hangen nesa.

“Mun bayyana ƙarara cewa ba mu fice daga APC ba, kuma ba mu da niyyar ficewa, jam’iyyar CPC ta kasance ɗaya daga cikin ginshiƙan jam’iyyar APC, kuma mun jajirce wajen jajircewarmu ga jam’iyyar da manufofinta na ci gaba.

“A matsayinmu na jam’iyyar da ta gada a cikin jam’iyyar APC, muna alfahari da sadaukarwar da aka yi wajen gina dandali da zai samar da haɗin kan ƙasa, adalci, da ci gaban ƙasa, ba za mu bari ɗaiɗaikun mutane su ruguza jam’iyyar da muka taimaka wajen ginawa ta tsawon shekaru da muka yi ba.

“ƙoƙarin haifar da rashin haɗin kai a cikin jam’iyya da ƙasa ba ya nuna ra’ayi ko matsayi na jiga-jigan jiga-jigan jam’iyyar CPC kuma ba za a amince da su ba.

“Mun amince da sauye-sauyen tattalin arziki da shugabanci da Shugaba Tinubu ke jagoranta, duk da cewa waɗannan manufofi na iya kawo ƙalubale, matakai ne masu muhimmanci na sake gina tattalin arzikinmu da kuma samar da makoma mai inganci ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya, muna roƙon haɗin kai yayin da alfanun su ke fitowa.

“Mun yarda cewa wasu mambobin jam’iyyar na iya jin cewa an ware su, amma irin wannan damuwar ba ta wata kungiya ce kadai ba, muna karfafa wadanda abin ya shafa da su nemi gyara ta hanyoyin da tsarin mulki ya kafa a cikin jam’iyyar, maimakon tayar da hankulan jama’a ko kuma ficewarsu cikin gaggawa.

“A wannan muhimmin lokaci a tafiyar dimokuraɗiyyar Nijeriya, dole ne dukkan ‘ya’yan jam’iyyar APC, musamman waɗanda ke da tushe a cikin kafa jam’iyyar, su haɗa kai don kiyaye abubuwan da ta gada da kuma tabbatar da dimokuraɗiyyar Nijeriya, dole ne a kauce wa ayyukan da ke kawo cikas ga haɗin kanmu da zaman lafiyar ƙasa.

“Muna kira ga shugabannin jam’iyyar APC da su ƙara cuɗanya da ‘ya’yan jam’iyya a dukkan matakai, ƙarfafa sadarwar cikin gida zai samar da haɗin kai, da rage zaman dar-dar, da kuma ƙara goyon bayan shirye-shiryen jam’iyyar. Dole ne a ci gaba da raya haɗin kan jam’iyya don ɗorewar nasarorin da aka samu a baya da kuma samar da makoma mai albarka.

“Saboda haka muna jaddada biyayyarmu ga jam’iyyar APC da kuma goyon bayanmu ga shugaba Tinubu. Iyalan CPC sun kasance ginshiƙin jam’iyyar APC kuma za su ci gaba da taka rawa wajen ci gabanta da kuma ci gaban Nijeriya

By ukarofi