Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kusa a Jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya ƙaryata jita-jitar da ke cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, yana shirin komawa jam’iyyar APC.
Galadima, wanda na hannun damar Kwankwaso ne ya ce NNPP na bai wa ’yan Nijeriya haske kan abin da jam’iyyar za ta iya bayarwa ta hanyar shugabanci nagari da na gaskiya, yana mai cewa ’yan siyasar da suka gaza ne kawai ke maganar zaɓen gaba tun kafin wa’adinsu ya ƙare.
A baya-bayan nan, Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi hasashen cewa Kwankwaso zai dawo APC, inda ya ce tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa yana shirin sauya matsayi.
Sai dai a wata hira da The Guardian, Galadima ya ce da ba don Shugaba Bola Tinubu ba, da babu yadda za a ce wani irinsa da ya taɓa zama gwamnan Kano zai zama shugaban jam’iyyar ƙasa.
Yayin da yake bayyana cewa ba wani mai hankali a Kano ko wani ɓangare na ƙasar da zai yi alfahari da dangantaka da APC a ƙarƙashin Ganduje, Galadima ya zargi shugaban jam’iyyar da ƙoƙarin amfani da NNPP don samun shahara a kafafen yaɗa labarai.
Ya ce: “Na fara jin wannan daga gare ku. To, idan muka koma APC, shin za a ji daga bakin Ganduje ne? Ko don shi kaɗai ma babu wanda zai so komawa APC. Tinubu ne kaɗai zai iya sa Ganduje ya zama shugaban jam’iyya.”
