Ba mu yi wa CBEX rajista ba – SEC

Spread the love

Hukumar kula da kasuwannin hannayen jari ta Ƙasa (SEC) ta bayyana cewa kamfanin Crypto Bridge Exchange (CBEX), wanda ake kira da ST Technologies International Ltd ko Smart Treasure/Super Technology, bai da rajista da hukumar don gudanar da kasuwancin kadarorin dijital a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar 17 ga Afrilu, 2025, SEC ta ce ta samu rahotanni daga kafafen yaɗa labarai kan ayyukan CBEX, inda kamfanin ke gabatar da kansa a matsayin dandalin cinikayyar kadarorin dijital tare da alƙawarin riba mai yawa a cikin ƙanƙanin lokaci.

SEC ta ce bincike na farko ya nuna cewa CBEX na amfani da hanyoyin talla don yaudarar jama’a da su zuba jari, duk da cewa ba su da izini daga hukumar. Haka kuma, kamfanin ya kasa biyan masu zuba jari kuɗaɗen su, sannan ya rufe ofisoshin sa ba tare da bayani ba.

Hukumar ta ce za ta haɗa kai da hukumomin tsaro don ɗaukar matakan doka akan CBEX da masu ruwa da tsaki a cikinta, bisa tanadin sashe na 196 na sabon dokar zuba jari da hannayen jari ta 2025 (ISA 2025).

Daraktan janar na SEC, Dr. Emomotimi Agama, ya ce sabon dokar ta ba su ƙarin ikon yaƙi da damfara ta yanar gizo da tabbatar da kariya ga masu zuba jari, musamman a fannin kadarorin dijital.

Ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da ƙarfafa kulawa da saka ido, duk da cewa tana maraba da sabbin fasahohi a bangaren hada-hadar kudi, amma dole ne su kasance a cikin tsarin da aka tsara domin kare amfanin jama’a.

By ukarofi