Kotun koli a Burtaniya ta yanke hukuncin cewa mazan da suka canza sheka zuwa mata ba su da damar kiran kansu da suna mata a ƙarƙashin dokar daidaito ta ƙasar.
Hukuncin, wanda alkalai biyar suka gabatar a ranar Laraba na iya samun ƙalubalanta daga ƙungiyar kare haƙƙin bil adama, wanda kuma tuni ke ƙara rura wutar kiraye-kirayen sake fasalin dokar don daidaito tsakanin dukka ɓangarorin.
Shari’ar, wani batu ne a cikin yaƙin ‘yancin jinsi, wanda ya samo asali daga ƙalubalanta daga ƙungiyar kamfen mai mahimmanci na kare martabar mata na Scotland (FWS).
Hukuncin da aka yanke, wanda ya ce ma’anar mace ta doka ta dogara ne akan jinsi na halitta, wani rauni ne ga masu fafutukar neman ‘yancin mata-maza, kuma zai iya haifar da sakamako mai tasiri kan yadda ake amfani da dokar a Biritaniya ga bambanta jinsi guda, daidaiton biyan albashi, da damar haihuwa.
Hakan ya biyo bayan taƙaddamar shari’a da aka kwashe tsawon shekaru ana yi kan ko za a iya ɗaukar mazan da suka canza sheƙa a matsayin mace a karkashin dokar daidaito ta Biritaniya ta 2010, wacce ke da nufin hana wariya. Hakan ya janyo zazzafar muhawara, kasancewar wasu na ganin yin hakan tauye haƙƙin matan da aka haifa a matsayin mata, wasu kuwa na ganin yin hakan shi ne daidai, kasancewar sun riga sun aminta da su ɗin mata ne ba maza ba.
Da yake sanar da hukuncin a ranar Laraba, mataimakin shugaban kotun, Lord Hodge, ya ce: “Hukuncin da wannan kotun ta yanke shi ne cewa sharuddan ‘mace’ da ‘jinsi’ a cikin dokar daidaitawa ta 2010 suna nufin mata da suke jinsin na halitta.”
Duk da haka, ya ƙara da cewa: “Muna ba da shawarar a guji karanta wannan hukunci a matsayin cin nasara na wata ƙungiya ko fifiko a cikin al’ummarmu ta hanyar cin zarafin wani, ba haka ba.” Ya ce hukuncin “ba ya haifar da illah ga mutanen da aka janye” saboda suna da kariya a ƙarƙashin dokokin nuna wariya da daidaito.
Lord Hodge ya fara shimfiɗar jawabin nasa ne da nuna dama da kuma haƙƙin da mata-maza suke da shi, tare da tabbatar da ƙyamar da hantar da ake yi masu a matsayin abinda bai dace ba, ya kuma bayyana mata-maza a matsayin “yan tsiraru masu rauni kuma galibi ana cin zarafin su.” A ɓangare ɗaya, ya bayyana mata a matsayin waɗanda suka sha gwagwarmaya shekaru aru-aru don samun daidaito.
Ya ƙara da cewa: “Ba aikin wannan kotu ba ne ta tsara manufofin yadda za a kare muradun waɗannan kungiyoyi” amma “tabbatar da ma’anar dokar da majalisar ta kafa.”
Ya buƙaci kotun ta yi shiru yayin da ake karanto hukuncin, saidai kotun ta karaɗe da surutu yayin da yake bayyana hukuncin. Yayin da ɓangaren masu fafutukar kare haƙƙin mata na For Women Scotland, suka fara tafi tare da rungume juna lokacin da aka ƙare sauraron hukuncin, alamun da ke nuna haƙarsu ta cimma ruwa.
