Ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato ta bayyana baƙin ciki kan kashe shanu 36 da guba da jikkata wasu 46 a Tafi Gana. Shugaban ƙungiyar, Ya’u Idris, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, inda aka baza ganyayyakin yalo’ da guba a wajen kiwo, wanda shanun suka ci suka mutu.
Ya bayyana cewa tuni suka kai rahoton lamarin ga hukumomin tsaro na Rundunar Sojoji ta GOC 3 Division, DSS da ‘yan sanda. Ya ƙara da cewa GOC ɗin ya ziyarci wajen domin ganin halin da aka shiga da idanunsa, kuma ya buƙaci makiyayan su kwantar da hankali yayin da bincike ke ci gaba domin gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.
Lamarin ya faru ne kwanaki biyu kacal bayan kisan mutane 52 da raunata wasu da dama a ƙauyen Zekki, wanda ke cikin ƙaramar hukumar Bassa. Al’ummar yankin na zargin makiyaya da hannu a wannan hari, zargi da ƙungiyar MACBAN ta musanta. Shugaban ya kuma bukaci ‘yan uwansa Fulani da su zauna lafiya su bar hukuma ta ɗauki mataki.
