Harin Ƙungiyar Mahmuda: Ƙungiyar ɗaliban Kaiama ta nemi agajin gwamnati

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ɓullar ƙungiyar mai suna Mahmuda, wadda wani tsagi ne na Boko Haram, ya haifar da barazana ga zaman lafiyar al’ummar da ke rayu a yankunan iyakokin Ƙananan Hukumomin Baruten da Kaiama na Jihar Kwara da Borgu a Jihar Neja, ganin yadda mayaƙanta ke kai hare-hare ga ƙauyuka.

Mayaƙanta sun kashe mutane da dama da garkuwa da wasu gami da ɗaiɗaita dukiyoyin al’umma, lamarin da ya jafe jama’a da dama cikin zaman ɗar-ɗar a yayin da hukumomin tsaro suka nuna gazawa wajen daƙile ayyukan ƴan ta’addar.

Don haka ne Ƙungiyar Ɗaliban Kaiama ta Ƙasa, a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Shugabanta na riƙon ƙwarya, Musakallah Muzammil ta hannun Sakataren riƙon ƙwarya, Idris Ibrahim, ta koka game da asarar dukiyoyi da rayukan al’umma da ake yi a ƙaramar hukumarsu ganin yadda ayyukan ƴan ta’addar ke ƙara ta’azzara.

Ta ce, al’umma a ƙauyukan Kamanji, Tenebo da Nuku suna fama da matsanancin rashin tsaro a sanadiyyar farmakin da mayaƙan suke kai masu.

Ƙungiyar ta kuma koka game da kalaman rundunar ƴan sandan jihar na ranar 19 ga watan Afrilu, 2025, inda ta ƙaryata batun cewa akwai ƴan ta’adda a shiyyar, ta na mai cewa ana nuna wa al’ummarsu wariya.

Saboda haka ne ta ke kira ga gwamnatoci a kowane mataki da su ɗauki mataki ta hanyar ƙarfafa jami’an tsaro da wadatattun kayan aiki, don ganin an tseratar da rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin da ma jihar baki ɗaya.

By Babaji