Zanga-zanga ta ɓarke a mahaifar gwamnan Katsina bayan hatsaniya da Yaran Raɗɗa

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Matasa sun fantsama kan titina a mahaifar Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗa, wato garin Raɗɗa na Jihar Katsina, biyo bayan taƙaddama da ta ɓarke tsakanin jami’an tsaron jihar da aka fi sani da ‘Yaran Raɗɗa’ da wani mazaunin garin Raɗɗa.

Lamarin ya faru ne bayan gardama ta kaure tsakanin wani matashi mai suna Mustapha Ahmad da kuma jami’an tsaron jihar, ( C-Watch), lamarin ya sauya salo zuwa hatsaniya tsakanin ɓangarorin biyu.

Zagazola Makama, mai sharhi kan sha’anin tsaro ya wallafa ce wa, a yayin rikicin Ahmed ya samu munanan raunuka.

Da farko an kai shi babban asibitin Dutsinma, sai dai daga bisani an kuma mayar da shi asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake Katsina duba da tsananin yanayi da yake ciki.

Lamarin ya harzuƙa mazauna Raɗɗa, inda a ranar 20 ga watan Afrilu, matasa da dama suka fantsama kan tituna don nuna fushinsu.

Matasan sun buƙaci mahukunta a kan su tsawata wa jami’an tsaron al’umma na jihar, waɗanda a cewar ma su zanga zangar jami’an na amfani da ikon da suke da shi wajen cin zarafin al’ummar yankin a duk lokacin da irin haka ya faru.

Sai dai ‘yan sanda sun yi gaggawar shiga tsakani don ganin lamarin bai cigaba da ƙazance wa ba. Babban jami’in ’yan sandan yankin (DPO) ya kwantar da hankalin matasan bayan ya yi jawabi ga waɗanda ke zargin an ci zarafinsu.

DPO ya roƙe su da su bar zanga zangar, su koma gidajensu don ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, ya kuma tabbatar ma su da cewa za a yi bincike game da ƙorafe ƙorafensu.

Kazalika, hakimin Raɗɗa Alhaji Kabir Umar Barebari shima ya buƙaci masu zanga-zangar su zauna lafiya, tare da yin alƙawarin miƙa kokensu ga hukumomin da suka dace domin warware matsalar ta su.

Bayan shiga tsakani, masu zanga-zangar sun watse cikin lumana.

By ukarofi