Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi ta kori wani babban malami, Dokta Usman Mohammed Aliyu, daga aikin jami’ar, biyo bayan binciken cin zarafin wata ɗaliba.
A cewar ATBU HERALD a wata sanarwa ta musamman da aka fitar ranar 22 ga Afrilu, 2025, an amince da korar shi ne a yayin taron majalisar na 96 da aka gudanar a ranar Juma’a, 11 ga Afrilu, 2025.
An yanke hukuncin ne bisa shawarar kwamitin ladabtarwa na manyan ma’aikatan da ta samu Dr. Aliyu da laifin rashin ɗa’a bayan gudanar da cikakken bincike.
Wasiƙar sallamar mai ɗauke da sa hannun babban mataimakin magatakarda na manyan ma’aikata, Abdullahi Sulaiman, ta bayyana cewa an samu Dr. Aliyu da laifin wata ‘yar alaƙa da wata ɗaliba mai suna Kamila Rufa’i Aliyu da ke sashen nazarin kimiyyar sinadarai, tsangayar fasahar injiniyanci.
“Daga baya majalisar ta amince da korar shi daga aikin jami’ar nan take, kuma an umurce shi da ya miƙa dukkan kadarorin da ke hannunsa ga shugaban sashensa da katin shaida ga babban jami’in tsaro jami’ar,” kamar yadda wasiƙar ta bayyana.
Sanarwar ta kuma yi karin haske da cewa an yi korar ne kamar yadda Babi na 3, Shafi na F, I, (o) na Sharuɗɗa na Ma’aikatan Jami’ar ya tanada.
A shekarar 2024 ne wata ɗaliba mai suna Kamila Rufa’i Aliyu ta kai ƙarar malamin ga hukumar gudanarwar Jami’ar, inda ta yi zargin cewa Dr. Aliyu na nemanta da lalata.
A ƙoƙarin da ya ke yi na ƙalubalantar zarge-zargen, Dr. Aliyu ya shigar da ƙarar Kamila da sashenta da kuma jami’ar a shekarar da ta gabata.
