Kotu ta ba EFCC izinin tsare ma’aikatan CBEX shida kan damfarar Dala biliyan ɗaya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A ranar Alhamis ne Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) izinin kamowa tare da tsare wasu masu tallata dandalin cinikayya na Crypto Bridge (CBEX) su shida bisa zargin zamba a hannun jarin da suka kai sama da Dala biliyan ɗaya.

Mai Shari’a Emeka Nwite, wanda ya bayar da wannan umarni bayan lauyan EFCC, Fadila Yusuf, ta gabatar da buƙatar, ya ce, za a ci gaba da tsare su har sai an kammala bincike kan laifuffukan da ake zargin su da aikatawa tare da gurfanar da su gaban kotu.

“Na saurari abin da lauyan EFCC ta gabatar. Saboda haka, an ba da izini kamar aka nema,” inji alƙalin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa mutanen shida da ake zargin sun haɗa da Adefowora Abiodun Olanipekun, Adefowora Oluwanisola, Emmanuel Uko, da Seyi Oloyede.

By ukarofi