Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya umarci jami’an tsaro su kama ‘yan daba da duk waɗanda ke da hannu wajen tayar da zaune tsaye a Minna, babban birnin jihar.
Bago ya bayar da umarnin ne bayan samun tashe-tashen hankula a birnin na Minna.
Umarnin nasa ya haɗa da kama mutanen da ke yawo da gashin dada.
Tuni dai gwamnatin jihar ta sanya dokar taƙaita zirga-zirgar mutane da baburan haya, domin magance rikicin ’yan daba da birnin ke fama da shi.
Lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar aaalla mutane goma, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Ya kuma ƙara da cewa wannan umarni ba wai ga ‘yan jihar ne da ba su ji ba ba su gani ba, sai dai ga waɗanda ke da hannu wajen kawo cikas ga zaman lafiya da tsaro a jihar.
Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su ba jami’an tsaro haɗin kai tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi a cikin al’ummarsu.
Sanarwar dai ta janyo cece-ku-ce daga jama’a, inda wasu suka yaba da irin matakan da aka ɗauka yayin da wasu kuma suka nuna damuwarsu game da abubuwan da ka iya haifar da take ‘yancin ɗan adam.
Duk da haka, gwamnan ya ci gaba da jajircewa, yana mai cewa, “Ba za mu iya naɗe hannayenmu ba yayin da masu laifi suka mamaye babban birninmu. Wannan lokaci ne da ya kamata mu ɗauki mataki, kuma dole ne mu yi aiki da ƙarfi.”
