Nasarawa: ’Yan bindiga sun kashe ango da garkuwa da amarya kwanaki 13 da aurensu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, a daren Laraba sun harbe wani mai sabon aure tare da yin garkuwa da matarsa ​​zuwa wani wuri da ba a san inda suke ba a Jihar Nasarawa.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Akaleku da ke ƙaramar hukumar Obi da ke kan titin Lafia/Markurdi.

A cewar wani ganau da ya zanta da Blueprint Manhaja ya ce, maharan sun mamaye gidan sabbin ma’auratan ne da misalin ƙarfe 11 na dare. Sun harbe mutumin kuma suka yi awon gaba da matar.

Mr. da Mrs Alu Anzaku sun yi aure a ranar 12 ga Afrilu, makonni biyu da suka wuce. Wataƙila sun kasance cikin hutun amarci, lokacin da maharan suka dira a gidansu.

A lokacin gabatar da wannan rahoto ‘yan uwa da masu tausayawa sun nuna damuwa, domin ba a ji komai game da matar ba.

A wani lamari makamancin haka, wani bala’i ya afku a al’ummar Uluoke da ke ƙaramar hukumar Etsako ta Yamma a jihar Edo yayin da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kashe wani Mista Friday Pius tare da sace matarsa ​​mai ciki tare da ‘yar uwarta.

An tattaro cewa ‘yan bindigar sun kashe mahaifin ‘ya’ya uku ne a ranar Litinin tsakanin ƙarfe 1 na dare zuwa 2 na dare.

Lamarin ya haifar da zanga-zangar da mata a cikin al’umma suka yi, inda suka yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da ta taimaka.

Matan sun kuma yi kira ga Sanata mai wakiltar mazaɓar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, Hon. Dekeri Anamero, ‘yan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Etsako ta tarayya da hukumomin tsaro da su kai ɗauki domin ceto su daga hannun waɗanda ake zargin makiyaya ne.

An ce wanda aka kashen yana barci ne a lokacin da ‘yan bindigar suka shiga gidansa suka kashe shi tare da yin garkuwa da ‘yan uwa.

Masu garkuwa da mutanen sun bar ‘ya’yan marigayin su uku, waɗanda aka same su suna kuka a cikin jinin mahaifinsu.

Wata majiya ta ce bayan harbe mutumin ya mutu, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da matarsa ​​mai juna biyu da ‘yar uwarta, inda suka tafi da su cikin daji.

“Mutane sun ji ƙarar harbe-harbe a kusa da gidan marigayin, amma sun tsorata babu wanda ya fito, lokacin da mutane suka zo daga ƙarshe bayan harbe-harben ya lafa, an tsinci gawarsa a cikin jini.

“Makisan sun tafi da matarsa ​​da ‘yar uwarta cikin daji har yanzu ba a same su ba, a halin yanzu ba a gano matar mai ciki da ‘yar uwarta ba,” inji shi.

A cewarsa, rundunar ‘yan sanda tare da haɗin gwiwar ‘yan banga da mafarauta sun yi ta shiga daji a wani yunƙuri na ceto waɗanda lamarin ya shafa.

Sai dai ta yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su kai ɗauki ga al’umma, saboda ba sa iya shiga gonakinsu.

By ukarofi