Masari, Barau da jiga-jigan ‘yan siyasa sun halarci auren Mawaƙi Rarara da Jaruma Aisha Humaira

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, tare da tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari, sun kasance cikin manyan baƙi da suka halarci bikin ɗaurin auren fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, da amaryarsa, Aisha Ahmad, wadda aka fi sani da Aisha Humaira.

Majiyar Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa taron ɗaurin auren ya gudana ne a yau Juma’a a birnin Maidugurin Jihar Borno, bayan idar da sallar Juma’a.

Dauda Rarara, wanda ya shahara wajen waƙoƙin yabon ƴan siyasa, ya angwance da Aisha Humaira, wacce ta daɗe tana yi masa amshin waƙa kuma shahararriyar jarumar ce a masana’antar Fim ta Kannywood da ta yi fina-finai da dama.

Majiyoyi daga kusa da ma’auratan sun bayyana cewa dangantakar su ta fara ne a matsayi na abokan aiki, sai dai a hankali ta rikiɗe zuwa soyayya mai ƙarfi, wanda a yau juma’a ta kai ga aure.

By ukarofi