
Daga BELLO A. BABAJI
Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi kira ga al’ummar Nijeriya da su daina mayar da hankali akan waɗanda ke sauya sheƙa daga PDP ko wasu jam’iyyu zuwa APC, a madadin haka su yi la’akari da abinda ake fuskanta na gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
A ranar 23 ga watan Afrilu ne Gwamnan Jihar Delta Sheriff Oborevwori da abokin tafiyar Atiku a zaɓen 2023, Ifeanyi Okowa da wasu ƴan PDP a jihar da suka koma APC.
Kamar haka Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC, ranar Laraba.
A yayin da ya ke tsokaci game da lamarin, Atiku a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya ce hakan ba baƙon abu bane a tsarin demokraɗiyya, wanda doka ta amince da shi.
Atiku ya zargi ƴan adawa da munafurci, wanda hakan abu ne da ke da mummunar tasiri ga tsarin tafiyar da shugabanci na gari.
Ya kuma kare suka da wasu ke masa bisa ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a lokacin bikin ƙaramar Sallah, inda ya ce ya yi hakan ne don girmamawa a gare shi a matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan ƙasa.
Haka kuma ya ce, zaɓen da ake fuskanta ba karawa ba ce tsakanin APC da PDP ko LP, batu ne na yin nazari game da gazawar gwamnati mai ci da ta jefa al’umma cikin tsananin rayuwa.
Kazalika, ya nemi ƴan Nijeriya da su yi watsi da ɓangaranci, ƙabilanci ko nuna banbancin addini, waɗanda da su ake amfani wajen kafa azzalumar gwamnati.
