Akpabio ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa jana’izar Paparoma

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaba Bola Tinubu ya aika da tawagar Nijeriya zuwa birnin Vatican domin halarta jana’izar Paparoma, wanda za a yi a yau Asabar, 26 ga watan Afrilu.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio shi zai jagoranci tawagar ta mutane biyar, kamar yadda Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya bayyana a wata takarda, ranar Juma’a.

Sauran mambobin tawagar sun haɗa da Ƙaramar Ministar Harkokin Waje, Bianca Ojukwu; Archbishop Luscius Ugorji; Archishop Matthew Kukah da kuma Archbishop Ignatius Ayua Kaigama.

A ranar 22 ga watan Afrilun 2025 ne Paparoma, wanda shi ne shugaban Cocin Roman Catholic ya rasu, bayan shafe shekaru 88 a duniya, kwana ɗaya bayan bikin Easter a Fadar Vatican.

Tawagar za ta gabatar da saƙon Shugaban Nijeriya na jajenta wa al’ummar kiristoci bisa babban rashin jagoran nasu.

Tun a ranar Litinin ne Shugaba Tinubu ya shiga sahun ƴan ɗariƙar Katolika da sauran Kiristoci wajen jimamin mutuwar Pafaroma a matsayinsa na jigo acikin al’umma.

By Babaji