
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sanda a Ogun, ta ce ta kama mutane uku da ake zargin su da hannu a haramtattun harkokin da suka shafi sassan ɗan-adam a yankin Itoju dake Abeokuta, babban birnin jihar.
Jami’arta ta hulɗa da jama’a, Omolola Odutola ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar a birnin.
Ta ce, a ranar 22 ga watan Afrilu ne jami’ansu suka kama wani mai suna Sunday Akintobi mai shekaru 36 da laifin safarar sassan jikin ɗan-adam a yankin.
A yayin faɗaɗa bincike ne kuma aka kama Oladimeji Olaniran mai shekaru 40 da Isiah Tijani ɗan shekara 38.
An samu sassan jikin ɗan-adam da wasu ƙasusuwa a gidan da aka kama su da wani waje da aka yi wa ɓadda-kama da sunan coci a birnin.
Ta kuma ce, kwamishinan ƴan sanda, Lanre Ogunlowo ya umarci Cibiyar binciken manyan laifuka ta jihar (SCID) da ta gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin tare da bayyana dukkan waɗanda suke da hannu aciki.
Haka kuma, ta yi kira ga al’umma da su riƙa bai wa jami’an ƴan sanda haɗin kai wajen samar masu da bayanai game da ababen zargi da ka iya zama barazana ga zaman lafiyarsu.
