Ribas: Wike ya bada sharaɗi bisa sulhunsa da Fubara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi watsi da batun cewa yana halin rashin lafiya ko kuma ya yanki jiki a wani taro.

Ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke ƙoƙarin kafa sharuɗɗan sulhu da abokin hamayyarsa kuma dakataccen Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara.

A yayin da ya ke magana a taron taya murnar zagayowar ranar haihuwar Hon. Ken Chikere a Fatakwal, Wike ya yi tsokaci game da matsalolin siyasar jihar, inda ya ce duk da cewa ƙofarsa a buɗe ta ke na yin sulhu, sai an samu dukkan ɓangarorin siyasar da lamarin ya shafa.

Wike ya ce, zaman lafiya bisa tabbas suke so ba rikici ba, amma sai an gayyaci mambobin majalisun dokoki na jihar da na ƙasa da kuma jam’iyyun APC da PDP.

Ya kuma ce, yaɗa sharri ta gidajen jaridu ba zai kawo ƙarshen rikicin ba, sai an amince tare da yin la’akari da maslahar al’umma da ta jihar.

A kwanakin bayan ne aka yaɗa cewa, Wike ya fita zuwa ƙasar waje domin neman lafiya, wanda ya musanta da cewa bikin yaye ɗansa a makaranta ya je.

By Babaji