An gano yadda matasan Ibo na ƙaurace wa shiga aikin soja

Spread the love

Daga MAHDI MUSA NUHAMMAD

Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana damuwarta kan yadda matasan ƙabilar Ibo ke ƙaurace wa aikin ɗaukar sabbin jami’an soja, inda ta danganta lamarin da ƙorafe-ƙorafe da aka daɗe ana yi.

Ya zuwa ranar Laraba mutane 200 ne suka yi rajista daga yankin Kudu maso Gabas, lamarin da ya sa rundunar sojin ƙasar ta yi kira ga matasan yankin da su yi amfani da wannan dama tare da cike kason ɗaukar jami’ai.

“Wannan shirin ya zama dole domin, kamar yadda bayanai suka nuna, mutane 200 ne kawai suka yi rajista daga Kudu maso Gabas, yayin da a wasu jihohi, ba ƙasa da mutane 4000”, inji shugaban ƙungiyar wayar da kan rundunar sojojin da ke hedikwatar rundunar, Anambra, Birgediya Janar hima Ekeator.

Da suke mayar da martani game da damuwar da Ekeator ya nuna, shugabannin Ibo sun bayyana cewa, illar yaƙin Biafra da kuma rashin adalci da ake ganin an yi wa yankin ya haifar da rashin yarda a tsakanin matasan Ibo da cibiyoyin gwamnatin tarayya ciki har da sojoji.

Da yake ba da jawabinsa, wanda ya kafa kuma shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar All Progressiɓes Grand Alliance, APGA, Cif Chekwas Okorie, ya bayyana cewa rashin sha’awar matasan ƙabilar Ibo ba wai a sojoji ne kaɗai ba ne, har da ‘yan sanda da sauran cibiyoyin gwamnatin tarayya.

Okorie ya ce “Abin baƙin ciki sai yanzu aka lura da lamarin, inda tun lokacin da aka kawo ƙarshen yaƙin Nijeriya da Biyafra abin ya faro.”

A cewarsa, bayan yaƙin basasa, ba a ɗauki matasa maza da mata ‘yan ƙabilar Ibo da suka nemi aikin yi kamar sauran ‘yan Nijeriya ba, kuma a wasu lokuta jami’an ɗaukar ma’aikata kan nemi cin hancin da ba zai yiwu ba daga masu neman ‘yan Ibo.

Hakan a cewarsa, ya sa matasa da dama suka daina sha’awar shiga aikin gwamnati, suna ganin cewa ayyukan gwamnati kamar ‘yan sanda da sojoji ba a yi musu ba adalci. “A hankali, Ndigbo ya fara neman wasu hanyoyin da za su iya samun aikin yi ban da cibiyoyin tarayya. Don haka, ban yi mamaki ba.”

By ukarofi