Ƙudajen zuma sun kashe manomi da raunata wasu da dama

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wasu gungun ƙudan zuma sun kai hari tare da kashe wani manomi, tare da raunata wasu biyu da munanan raunuka a gonar Olobe da ke Igbajo a jihar Osun.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 18 ga Afrilu, 2025.

Marigayin, Abideen Olabiyi, wanda ya fito daga harabar Alalade, Ada, yana aikin gona tare da Solomon Kingsley da Olusegun Alalade a lokacin da zumar ta afka musu.

Rahoton ‘yan sanda daga sashin Otan-Aiyegbaju na rundunar ‘yan sandan jihar Osun wanda shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce: “A yau Juma’a 18/04/2025, da misalin ƙarfe 1645, an samu ƙorafi daga wani Babasanjo Alalade, namiji da ke zaune a unguwar Alalade Ada, jihar Osun, inda ya bayyana cewa ‘yan uwansa uku sun je gona, ɗaya Abideen, da Cif Olusegun Alalade, Sarkin Alalade, da Olusegun Adade magidanci, inda zuma ta afka musu a gonar Olobe Igbajo.”

Rahoton ya nuna cewa an ajiye wanda ya mutu a ɗakin ajiye gawa na asibitin Paradise Ikirun domin bincike.

Mutanen biyu da suka tsira a halin yanzu suna samun kulawa a wani asibitin da ba a bayyana ba a garin Ada na jihar Osun, inda aka ce halin da suke ciki ya tsananta.

“Lokacin da suka isa gonar wasu gungun ƙudar zuma ne suka kai musu hari a sakamakon haka Abideen Olabiyi ya rasa ransa yayin da sauran biyun suka yi nasarar tserewa da rayukansu, amma jami’an tsaro na bincike bayan sun ziyarci wurin da lamarin ya faru.

By ukarofi