Yadda uba da ɗa suka mutu yayin tsaftace madatsar ruwa a Bauchi

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ma’aikatan Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Bauchi guda huɗu sun rasu a yayin da suke aikin tsabtace madatsar ruwa ta Gubi.

Mummunan lamarin ya afku ne da misalin ƙarfe 5 na yammacin ranar Asabar a lokacin da suke gudanar da aikin tsaftace ruwan.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil ya fitar, ya bayyana cewa: “An fara aikin tsaftace madatsar ruwan ne da misalin ƙarfe 12:00 na safe, a lokacin da ake aikin ne ma’aikatan suka shiga cikin na’urar domin su kwashe bututun madatsar, amma tsautsayi ya same su, daga bisani kuma aka ɗauke su a mace.

Marigayan dai an bayyana sunansa da Shayibu Hamza mai shekaru 48; Abdulmalik Yahya, 29; Jamilu Inusa, 29; da Ibrahim Musa, mai shekaru 42 – dukkansu mazauna kauyen Firo, al’umma ne da ke kusa da madatsar a ƙaramar hukumar Ganjuwa ta jihar Bauchi.

Daga cikin waɗanda abin ya rutsa da su har da uba da ɗansa, kuma ‘yan uwa sun ce za a ɗaura auren ɗan ne nan da makonni biyu.

Wani abokin aikinsu ya bayyana cewa; “Abin ya faru ne a lokacin da suke aikin tsaftace ruwan da ake kula da ruwan da ake yi wa babban birnin Bauchi. Na samu labarin suna cikin tafki, sai suka ga wasu kifaye a cikin ruwan datti, ɗaya daga cikinsu yana ƙoƙarin kama kifi, kifin ya yi zurfi, sai ya bi shi ya mutu.

“Ana cikin haka, wani abokin aikinsa da ya ga abin da ya faru ya yi ƙoƙarin ceto shi, shi ma ya mutu, kuma anyi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ta tanada.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Bauchi, CSP Mohammed Ahmed Wakil ya ce ma’aikatam da suka rasu sun hada Shayibu Hamza mai shekaru 48 da Abdulmalik Yahya mai shekaru 29 da Jamilu Inusa mai shekaru 29 da kuma Ibrahim Musa mai shekaru 42.

Ya ci gaba da cewa, lamari mai ban tausayi ya afku a madatsar ruwa ta Gubi, wanda ya yi sanadin asarar ma’aikatan da suka sadaukar da kansu a yayin wani aikin yashe shara da ke cikin ramuka a madatsar ruwan ta Gubi.

Ya ce, a lokacin da waƙi’ar ta afku, an yi ƙoƙarin ceto su, aka fito da su a sume daga cikin ramin tara ruwan da suke aikin, daga nan aka garzaya da su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa ɓalewa da ke Bauchi, amma duk da kulawar gaggawa da aka ba su, sai Allah Ya karɓe su, likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.

Wakil ya ce, a lokacin da ’yan sanda suka samu labarin faruwar lamarin, sun tura jami’ai zuwa wurin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don gano ainihin abin da ya faru.

Ya ce, akwai buƙatar ƙara ɗaukan matakai a ɓangaren kula da ruwa, yana mai jaddada muhimmancin dukkan ma’aikatan su kula da bin ƙa’idojin aminci da aka kafa don rage haɗari nan gaba.

By ukarofi