
Daga BELLO A. BABAJI
Kimanin mutane 30 da suka haɗa da mata da yara ƙanana ne suka rasu a yayin da wata mota ƙirar Bus ta taka wani abin fashewa da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne suka dasa a Borno.
Abin fashewar ya tarwatse ne a lokacin da wasu motoci ke kan hanyar tafiya Gamboru-Ngala dake yankin Tafkin Chadi.
Mata huɗu ne suka rasa rayukansu a lamarin, wanda ya auku a ranar Litinin, yayin da yara shida suka rasu da kuma sauran matafiya.
Lamarin ya kai adadin waɗanda suka rasa rayukansu a harin bom na Kala Balge zuwa 16.
Tuni aka garzaya da waɗanda suka samu raunuka zuwa asibitocin Gamboru Ngala da Rann don ba su kulawa.
Haka ma, a ranar ne aka kashe wasu mutane da dama yayin da wasu suka samu raunuka a yayin harin da aka kai wa wasu mutane da ke addu’a bisa rashin ɗaya daga cikin jagororin al’umma a wani ƙauye da ke Ƙaramar Hukumar Chibok.
Ana zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram da aikata ta’addancin wanda a ranar Lahadi ma suka kashe wasu jami’an haɗaka na Civilian JTF a yankin Hawul dake jihar da Garkida a Jihar Adamawa.
