Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina, a Jihar Katsina ya raba kayan sana’a ga al’ummar mazaɓar sa na sama da Naira miliyan 500.
Kayan tallafin ya haɗa da motoci 24,babura 150, keken ɗinki 150 ,injinan ban ruwa na noman rani 150, injinan markaɗe 50,takin zamani guda 300,injinan feshin a gona guda 60 da kuɗi Naira miliyan 60.
Waɗanda suka amfana da tallafi sun haɗa da shugabannin jam’iyya da matasa,mata, ƙungiyoyi da jami’an tsaro a ƙaramar hukumar ta Katsina.
Gwamna Dikko Raɗɗa wanda ya ƙaddamar da bada tallafin,ya ce wannan yana cikin tsare tsaren gwamnatin sa na tallafawa al’umma ƙarƙashin shirin bunƙasa cigaban al’umma.
Ya ce wannan tallafi bashi ne na farko da ɗan majalisar ya bada ba ,akwai ayyukan hanyoyi da yake samarwar a cikin ƙaramar hukumar Katsina.
A na shi jawabin ɗan majalisa Hon Sani Ɗanlami ya ce ya samar da wannan tallafi domin taimaka ma ƙoƙarin da gwamna Dikko Raɗɗa ke yi na tallafawa al’umma.
Ya yabawa gwamnan bisa ƙoƙarin da yake yi na daƙile matsalar tsaro a jihar.
Taron da ya gudana a filin wasa na Sarki Muhammadu Dikko a garin Katsina ya sami halartar kakakin majalisar dokoki na Jihar Katsina da mataimakin sa tare da wasu ƴan majalisar dokokin jihar.
