Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda mai kula da ayyuka na hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta Abuja, Ari Muhammed Ali, wanda ya yi ritaya a watan Maris na 2025, ya koma jam’iyyar APC kuma yana neman tsayawa takarar ɗan Majalisar Dattawa a zaɓen 2027 mai zuwa.
An sallami tsohon DIG daga aiki ne tare da DIG Dasuki Galandachi, Rhoda Adetutu Olofu, Jonathan Towuru (mai wakiltar shiyyar Kudu-maso-Kudu), Suleiman Yusuf, Banji Lawal Badru, da Bala Ciroma bisa zarge-zargen ƙara shekaru da kuma karya dokokin hidima.
Kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito, DIG Ari Muhammed ya koma jam’iyyar APC, kuma a yanzu yana sa ran tsayawa takarar Sanata a shekarar 2027.
“Ari Mohammed dai yana takarar Sanata ne a ƙarƙashin jam’iyyar APC a yankin Nasarawa ta Kudu,” wata majiya ta ce.
A Nasarawa, DIG Ari Muhammed (mai ritaya) da alama yana bin sahun tsohon Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Mohanmed Abubakar Adamu, wanda ya yi ritaya a shekarar 2021 kuma ya bayyana burinsa na tsayawa takarar gwamna a jihar gabanin zaɓen 2027.
Adamu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan jihar Nasarawa a hukumance a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Adamu wanda ya riƙe muƙamin IGP daga shekarar 2019 zuwa 2021 a ƙarƙashin gwamnatin Muhammadu Buhari, ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da mambobin kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC na jihar da aka gudanar a garin Lafia.
Tsohon IGP ɗin ya ce ya yanke hukuncin ne sakamakon kiran da mutanen Nasarawa suka yi masa.
A cewarsa, mutane sun yi yarda da iya shugabancinsa da gogewarsa.
Adamu ya yi alƙawarin tafiyar da gwamnati ta kowa da kowa kuma mai son jama’a idan aka zaɓe shi a matsayin gwamna.
“Ina amsa kiran jama’ata da suka yi imanin zan iya yin hidima da ciyar da Nasarawa gaba.
“Gwamnatina, da yardar Allah, za ta kasance cikin haɗin kai, da gaskiya, tare da mai da hankali wajen samar da ci gaba mai ma’ana a dukkan ɓangarori,” inji Adamu.
A halin da ake ciki, sanarwar nasa ta ƙara wani gagarumin suna a jerin masu neman tsayawa takarar gwamna a 2027.
Gwamna Abdullahi Sule, wanda shine gwamna mai ci, yana kan karagar mulki a karo na biyu a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
