Gwamnatin Tarayya ta umarci WAEC da NECO su rungumi tsarin kwamfuta

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta umurci Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare a Yammacin Afrika (WAEC) da kuma Hukumar Shirya Jarrabawa ta ƙasa (NECO) da su rungumi cikakken tsarin jarrabawar na’urar kwamfuta a dukkan jarrabawarsu nan da shekarar 2026.

Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa ne ya bayyana haka a lokacin sa ido kan jarrabawar da ake yi tare da jami’an JAMB, a Bwari ranar Litinin.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, sama da mutane miliyan 2 ne suka yi rajista domin gudanar da jarrabawar a cibiyoyi sama da 800 a faɗin ƙasar.

Dakta Tunji ya yaba da tsarin CBT da ya gani a cibiyoyin hukumar daban-daban a Nijeriya yayin da ɗalibai suke rubuta jarrabawa, lamarin da ya ce ɗaya ne daga cikin ababen da za su taimaka wajen inganta al’umma, kamar yadda ya ke a tsarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Ya ƙara da cewa, jarrabawar WAEC da NECO da za yi a watannin Mayu da Yunin 2026 za a yi su ne baki ɗaya ta komfuta, saɓanin a takarda da ake yi baya.

A cewarsa, hakan zai taimaka wajen samar da nagartattun ɗalibai da za su yi gogayya da sauran ɗalibai a kowane mataki na karatu s duniya.

By ukarofi