Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP a Nijeriya, Sule Lamido, ya yi gargaɗin cewa ƙoƙarin rusa jam’iyyar tamkar yunƙurin murƙushe dimokaraɗiyya ne.
Sule Lamido, wanda tsohon ministan harkokin waje ne, ya ce ficewar wasu jiga-jigan PDP zuwa APC mai mulki tuggun ne da ba zai yi wa ’yan siyasa daɗi ba nan gaba.
“Murƙushewa da gana azaba, su ne alamun cewa mulki ya zo, haka abin yake a tarihi,” inji shi cikin wata hira.
“Ya kamata a ce Shugaba Bola Tinubu ya yi adalci, ya san cewa shi shugaban kowa da kowa ne, ya ƙyale mu mu ‘yan siyasa mu yi kokawa da APC a jam’iyyance. Amma idan bai yi hankali ba dabarar za ta ci shi.”
Lamido ya zargi shugaban ƙasa Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki da amfani da makaman jihar domin raunana jam’iyyun adawa.
Ya yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da yin hakan ba tare da la’akari da hakan ba, ba wai kawai zai lalata tsarin dimokuraɗiyya ba ne, har ma a ƙarshe ya cinye waɗanda suka kitsa ta.
“Idan APC a matsayinta na jam’iyyar siyasa ta yi faɗa da PDP, wannan al’ada ce, amma idan gwamnatin tarayya ƙarƙashin jam’iyyar APC ta yi amfani da cibiyoyin ƙasa wajen yaƙar ‘yan adawa, hakan yana da haɗari, ba ‘yan APC ne kaɗai ke fada da mu ba, gwamnati ce da kuma shugaban ƙasa da kansa.
“Yin amfani da Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) da sauran hukumomi wajen tsoratarwa da raunana jam’iyyun adawa ya kai ga halaka kansu, waɗanda suka shiga APC saboda tsoro za su yi nadama a ƙarshe.”
Ya yi nuni da cewa Tinubu ya yi imanin cewa yana tabbatar da makomarsa ta siyasa ne ta hanyar raunana jam’iyyar PDP. Sai dai ya jaddada cewa, abin da Shugaban kasa bai gane ba shi ne, ta hanyar yin hakan, yana raunana Nijeriya da kanta.
Lamido ya ce an gina dimokuraɗiyya akan ‘yanci, ‘yanci, da kuma sahihin adawa. “Idan kuka lalata ‘yan adawa, kun lalata al’umma,” inji shi.
Ya kuma ƙara da cewa, tsoron cin zarafi da hukumomi irin su EFCC ke yi na tilastawa ’yan siyasa da dama shiga abin da ya bayyana a matsayin kawancen kashe-kashe da jam’iyya mai mulki, yana mai hasashen cewa a ƙarshe ruɗani zai sa mutane da yawa su koma PDP.
A ranar Litinin Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oboreɓwori, da wanda ya gada Ifeanyi Okowa suka koma jam’iyyar APC a hukumance bayan sun bar PDP.
A baya-bayan nan wasu ‘yan majalisa daga jam’iyyun adawa na Labour da NNPP sun koma APC ɗin, yayin da ake raɗe-raɗin wasu gwamnonin na kan hanyar komawa APC ɗin.
