Amurka ta kama ’yan Nijeriya 22 da ake zargi da damfara da hotunan batsa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A wani samamen ƙasa da ƙasa, hukumar FBI ta sanar da kama wasu ’yan Nijeriya 22 da ake zargi da hannu a zamba ta intanet wacce ta jawo mutuwar matasa da dama.

An gudanar da samamen ne ƙarƙashin Operation Artemis, inda hukumomin Nijeriya, Amurka, Kanada, Ostiraliya da Birtaniya suka haɗa kai wajen zaƙulo waɗanda ke da hannu a lamarin.

Binciken da aka gudanar cikin kusan shekaru biyu ya gano yadda masu aikata laifin ke amfani da kafafen sada zumunta wajen yaudarar matasa.

‘Yan damfarar na samun hotunan tsiraicin matasa a faɗin duniya, sannan su yi amfani da su wajen tsoratar da su da kuma karɓar kuɗi.

Binciken ya nuna cewa waɗanda ake zargin suna fakewa a matsayin matan da ke son abota a intanet domin samun damar karɓar hotunan batsa daga matasan.

Bayan samun hotunan, suna fara barazanar fallasa su idan ba su biya wani adadin kuɗi ba, kuma ko bayan biyan kuɗin, barazanar kan ci gaba har zuwa kai ga matasan su ɗauki rayukansu.

Wata jami’ar FBI, Karen R., ta bayyana cewa wannan laifi ba wai kawai damfara ba ne, illa ce kai tsaye ga rayuwar matasa masu tasowa.

A shekarar 2023, FBI da jami’an ‘yan sanda na Kanada da Ostiraliya sun kafa sansanin wucin gadi a Legas tare da haɗin gwiwar hukumar EFCC domin samame.

Kwamandan EFCC, Michael Wetkas, ya ce fahimtar yanayin Nijeriya ya taimaka matuƙa wajen nasarar samamen.

Wayoyin da aka kwace daga hannun waɗanda ake zargin sun bayyana hujjojin bayanai da hotuna da suka gamsar da cewa sun aikata laifin. 

Hukumomin Amurka sun ce samamen ya aika gagarumin sako ga matasa da ke neman shiga harkar damfara ta intanet cewa dubunsu za ta cika a kwana a tashi.

Michael Erɓin daga ofishin jakadancin Amurka a Legas ya bayyana cewa za su ci gaba da bincike da kuma nemo sauran waɗanda ba a kama ba.

By ukarofi