Na yi nadamar take wa Atiku baya a 2023, inji Okowa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Gwamnan Jihar Delta, Dr. Ifeanyi Okowa, ya ce, ya yi nadamar tsaya wa takara a matsayin mataimaki ga Atiku Abubakar a zaɓen sShugaban ƙasa na 2023, inda ya ce, hakan ya saɓa wa shiyyarsa da kuma muradin mutanensa.

A wata hira da aka yi da shi a shirin safe na gidan Talabijin na Arise, Okowa ya yarda cewa da yawa a jihar Delta da kuma Kudu ba su ji daɗin wani shugaban arewa ba bayan shekaru takwas da Muhammadu Buhari ya yi yana mulki.

“Ko a lokacin da muke yakin neman zaɓe, na gane mutanenmu ba su da sha’awar a ce wani ɗan Arewa ya hau mulki.

Ya kuma maida martani ga tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki kan sukar ficewar sa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Okowa, wanda abokin takarar tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ne a zaɓen 2023, ya bayyana cewa Saraki ba shi ikon sukar sauya sheƙarsa.

Sanata Okowa ya ce, sun yanke shawarar sauya sheƙa ne bayan shawarwari da suka ɗauki watanni suna yi, da kuma gajiya da halin da jam’iyyar PDP ke ciki.

Okowa ya kuma tabbatar da jita-jitar da ke cewa ɗan takarar shugaban ƙasan na PDP a 2023 yana nazarin sauya sheƙa.

“Na tattauna batun haɗakar ’yan adawa da Atiku kafin mu sauya sheƙa zuwa APC, kuma yanzu haka yana kan hanyarsa ta ficewa daga jam’iyyar PDP,” inji Ifeanyi Okowa 

Okowa ya nesanta kansa daga haɗakar ’yan adawa da Atiku ke ƙoƙarin jagoranta, yana cewa babu cikakken tsari, hangen nesa a cikinta.

“Alamu sun nuna cewa har yanzu babu wani sahihin dandali da haɗakar za ta koma, kuma ba abin da ke nuna cewa haɗakar za ta iya yin ƙarfi cikin ƙanƙanin lokaci.”

Maimakon haka, Okowa ya nuna goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai kiran a bar shi ya kammala wa’adin mulkinsa na shekaru takwas.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa sake zaɓen Tinubu a 2027 zai tabbatar da adalci a tsarin karɓa-karɓa na shugaban ƙasa tsakanin yankuna, kuma zai fi amfanar Nijeriya.

By ukarofi