Minista Goronyo ya jagoranci bada ba’asi kan nasarorin gwamnati a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Ma’aikatar Ayyuka ta shirya zaman nazarin ayyukan da aka aiwatar a zangon farko na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, waɗanda aka cimma ƙaddamarwa a taron Majalisar Ayyuka ta Ƙasa karo na 29.

An gudanar da taron ne na kwana uku a Gidan Gwamantin Jihar Nasarawa dake Lafiya, inda aka samu halartar manyan sakatarori da sauran masu-ruwa-da-tsaki kan harkokin ayyuka da sauran ababen more rayuwa domin nazarin nasarar da aka samu a ci-gaban samar da tituna a Nijeriya.

Da ya ke jawabi, Kwamishinan Ayyuka, Gine-gine da Sufuri na jihar, Mu’azu Adamu Gosho ya yaba wa dukkan masu-ruwa-da-tsaki bisa aiki tuƙuru da jajircewa da suka nuna yayin da aka samu nasarori wajen kammala ayyuka da dama da aka sa a gaba.

Ya yi kira a gare su da su ƙara zarge damtse wajen tabbatar da ayyuka masu nagarta a ɓangaren gina tituna a sassa daban-daban na Nijeriya.

A nasa jawabin, Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya kuma Shugaban taron, Injiniya Olufunso Adebiyi ya yi godiya ga Ministan Ayyuka, Dave Umahi da ya bada izinin taron, ya na mai cewa hakan wani mataki ne da ke nuna hanyoyin da suka bi wajen cimma nasarori a yayin sauke nauyin da aka ɗora musu.

Ya kuma ce, za su cigaba da aiki tuƙuru wajen tabbatar da aiwatar da ayyukan ababen more rayuwa ga al’ummar Nijeriya a ƙarƙashin tsarin Shugaba Bola Tinubu na sabonta ƙasa a gare su.

By Babaji