Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gidauniyar GwaGware ta nemi uwar jam’iyar APC a Jihar Katsina da ta hukunta mataimakin shugaban jam’iyar na jiha Bala Abu Musawa bisa kalaman cin mutuncin ga gwamna Dikko Raɗɗa.
A wata takardar koke ɗauke da sa hannun shugaban gidauniyar da uban ƙungiyar Yusuf Ali Musawa da Kabir Usman Amoga suka aikewa shugaban jam’iyar APC a jihar sun bayyana cewa Bala Abu Musawa yayi wannan kalaman a taron ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina.
Sai dai takardar ba tai wani cikakken bayani game da kalaman da suke zargin mataimakin jam’iyar yayi ba ,amma bai rasa nasaba da cikakken gwamnan da yayi bayan da gwamnan yazo taron a makare.
A wajan taron Bala Abu Musawa ya faɗawa gwamna Dikko Raɗɗa da ya nemi afuwa daga mutanen da suka shafe awonni suna jiran gwamnan a matsayin sa na babban baƙo.
Sai dai a amsar da gwamnan ya bayar ya nuna cewa shi lokacin da aka bashi na zuwan shi wajen taron a lokacin yazo amma tunda jam’iyar APC ta buƙaci ya nemi afuwa mutane da suka je taron sai yace ya nema da jama’a suyi haƙuri.
Wannan gidauniya gwamna Dikko Raɗɗa ya kafa ta bayan da Sarkin Katsina ya bashi sarautar Gwagwaren Katsina.
