Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Shugaban ƙasa Tinubu ya gargaɗi masu yunkurin wargaza ƙasa da masu ƙoƙarin haɗa kai da su da cewa gwamnati ba za ta lamunce masu ba.
Yayi gargaɗi ne da yake ganawa da sojoji a filin jirgin sama na tunawa da Umaru Musa Yar’adua a Katsina.
“Wannan wani muhimmin lokaci ne da yakamata a murƙushe dukkan masu ƙoƙarin tayar da ƙayar baya da masu mara masu baya”inji Tinubu.
Ya yaba da ƙoƙari da jajircewa wajen yaƙi da yan ta’adda inda ya kwatanta su a matsayin masu kare tsarin mulkin Nijeriya.
Bola Tinubu ya bayyana ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi na samar da makamai da horas wa na musamman da sauran kayan aiki don a ƙarfafa masu gwiwa wajen gudanar da aikin su.
Shugaban ya kuma basu tabbacin za a cigaba da kulawa da walwalan su da kuma biyan haƙƙoƙin su akan kari.
Ya basu tabbacin cewa za a samar masu da muhalli da kuma tallafi daban daban da kuma ƙarin albashi don su ƙara ƙaimi wajen tsaro da kariya ga ƙasa.
“Yakamata jajircewar ku ya fito fili ta yadda maƙiyan Nijeriya za su san cewa ba su da sauran saƙat, Yakamata jarimtar ku da kuma horon da kuke samu ya nuna ta fuskar ƙaruwar tsaro a faɗin dukkan sassan ƙasan nan”inji shugaba Tinubu.
